Zamantakewar Auren Hausa Fulani a Yau

Rayuwar Fahimtar Juna da Sanin Juna::
Na san wasu zasu ce dama basu Fahimci Juna ba,kuma basu san Juna ba,akayi Auren? A'a Sam! Shi wannan Matakin na Sanin Juna da Fahimtar Juna, wani mataki ne da yake Sanɗa Cikin Gidan Aure irin na Yau,bayan Matakin Rayuwar ANGO DA AMARYA,Wani Mataki ne me Sarqaqiyar Gaske,wanda da yawan Ma'aurata a yau daqyar suke iya tsallake shi,wasu Kuma sai Auren ya ɓalle(Rabuwa),wasu kuma Farinciki,walwala,kwanciyar Hankali,daga wannan Matakin yake Qaura tsakaninsu,sai a koma zaman Doya da Manja,amma JARUMAN Gaske suna iya tsallake shi harma suci ribar shi.
Rayuwa ce wacce a lokacin za'a Fahimci an ɗauki Auren Ibadah ne ko anyi sane domin Sha'awa,Birgewa ko ya kamata nayi,ko kuma wane da wane sunyi nima sai na yi ,ko kuma nayi ne don Huce taqaici,ko kawai dai na yi shine don naga anayi,ko kuma na yi sane don na gaji da Gorin da ake min?.???
Mataki ne wanda idan ba don Ibadah kayi ba ,wa Billah sai ka yi sa'ar Gaske zaka sha,ko da kasha zaka zamo cikin masu Kokawa da Auren,wala Mace wala Namiji,sai kaji kamar ka Gudu kabar Ladanka ,saboda idan don Sha'awa kayi zata gushe,idan don Birgewa kayi zaka Gaji da Kallon abin dake Birge kan kuma zaka ga babu waɗanda kake son ka burge ɗin a cikin Gidan,idan Huce takaici ne zaka fara jin komai ya wuce ,zaka fara jin me yasa ma nayi hakan? Da sauran saqar Zuciya mara Amfani,Amma wanda yayi domin Allah,domin Qauna ta Gaskiya,shine ya MORE
Mataki ne da Mace da Namiji suke Sanin Halin Juna me kyau da mara kyau,kuma zasu gansu a zahiri,babu yaudara,babu kara,babu ya Kamata,babu Algus,indai akwai Halin da Ɗabi'ar a tare dasu dole-dole,ko ba daɗe ko Bajima sai ya fito,wala Ɗabi'a ce wacce Hatta Iyayensu basu sansu dashi ba,wala me kyau ko mara kyau dole sai ya fito,idan ma sun aro wata Ɗabi'a ce da ba tasu ba kafin Aure,aka samu aka rufa akayi dole fa ta usil ɗin sai ta fito,shi yasa yawancin matakin yafi zuwa bayan Shekara 2,3,4,5 da Aure wasu suna iya Takawa har Izuwa 10 kafin komai ya gama Fallasa ya gama fitowa sosai da Sosai.
Mataki ne da Mace zata ce a ranta,dama wane haka yake,dama har ya kai haka? Wasu ma Ɗabi'un su bata mamaki matuqa gami da Al'ajabi,haka shima Namijin zai dinga ji,har wani ma ya nemi ya rasa inda zai tsoma Kansa saboda Mamaki da Tunani,Amma idan akayi Haquri aka jure,aka zauna aka zana,aka Bayyana Kuskuren,idan akayi Katari akwai Kusanci me kyau,sai a samu sauqi da maslaha a lamarin har akai ga mataki me Daɗi ,Idan ba wannan kuma sai hura hanci,sai faɗa,sai Rabuwa ko Tashin Hankali a tsakani. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C