'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 18 a Gidan Biki a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna a Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 18 da kuma jikkata wasu 30 a gidan biki.
An kai harin ne a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna kan masu bikin aure a kauyen Kukun-Daji.
Lamarin dai ya faru ne a jiya Lahadi da tsakar dare. Bayanai na cewa ango da amaryar da ake bikinsu, sun tsira daga harin.
Wani shugaban al'umma daga yankin Kaura, Jonathan Asake ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun bude wuta ne yayin da mutane ke ta cashewa, sannan daga bisani suka tsere.
Jonathan ya ce nan take mutum 15 suka mutu - sauran uku kuma sun mutu ne a asibiti lokacin da ake ba su kulawar gaggawa.
Shin 'yan Boko Haram ne suka kashe sojoji a Katsina?
'Taƙaddama ta ɓarke tsakanin kwastan da al'ummar Jibia'
Kakakin 'yan sanda a jihar ta Kaduna, Muhammad Jalige ya tabbatar wa BBC da kai harin, amma bai yi karin haske kan adadin mutane da aka kashe ba.
Sai dai yana mai cewa hukumomi na tattara bayanai, ya kuma kara da cewa suna iya kokarinsu don tabbatar da tsaro a jihar.
An sha kai irin wannan muggan hare-hare a kan babura a jihohi da dama da ke arewa maso yammacin Najeriya, tare da kashe ko sace mutane don neman kudin fansa wani lokaci a kwashe musu dukiyoyi.
A ranar Asabar ma, an kashe akalla jami'an tsaro 16 ciki har da manyan hafsoshi uku yayin da suka yi kokarin kutsawa cikin wani daji da 'yan fashi ke mafaka a jihar Katsina.
Sojojin Najeriya sun ce sun yi nasarar kashe mutum 17 daga cikin 'yan fashin a lokacin musayar wuta.
Sama da mutum dubu takwas ne suka rasa rayukansu sakamakon irin wadanan hare-hare a cikin shekaru 10 a yankin arewa mao yammacin Najeriya. 

Source: BBC hausa

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C