Turkashi_Duk Masu Son Aurena Sai Sun Bukaci Yin Zina Dani

Malam wallahi lamarin nan na matukar daure mini kai. Kuma na rasa yadda zanyi shi yasa nace zan nemi shawara wajen masu karatu ko zan samu mafita.
Shekaruna 23 da haihuwa. Mu biyar uwar mu ta haifemu. Nice ta uku kuma nice mace tilo da aka haifa.
Mahaifinmu ba mai kudi bane can, amma kuma babu abunda muka rasa na rayuwa. Wasu ma da suke mana kallon nesa suna mana ganin masu kudi ne sosai saboda yadda muke rayuwar mu.
Tun ina karama nake da masoya, amma kuma a lokacin dana cika mace a wannan lokacin ne masoya da kuma masu sona da aure suka kara yawaita.
Ina daf da kammala karatun sakandare nane ne na hadu da wani saurayi. Wanda ya nuna mini so da kauna. Babu irin hidimar da baya mini ganin yaro ne amma kuma yana da sana'ar da yake yi. Don haka matsalar kudi bai sansu ba.
Soyayyar mu ya kai har gaban iyaye, aka umurce ya fito a daura mana aure, ya kuma amince yace a bashi dan lokaci ya shirya iyayena suka aminta.
Sai dai na lura tun daga wannan lokacin ya rage zuwa wajena, ya rage kirana kamar yadda ya saba. Nakan bashi uzuri da tunanin yana da aiyuka ne a gaban sa. Amma daga baya sai na fahimci duk rashin lokacinsa ba zai rasa lokacin da zai kirani ba ko ya tura mini sakon tex.
A wani yammacin ranar Juma'a ne ya zo wajena, muka yi hira sosai. Anan ne na samu damar tambayar sa ko mai yasa ya sau lokaci haka bai nemi ne ba. Amsar daya bani bata gamsar dani ba,. Amma dai hakan na hakura. A wannan lokacin ne kuma ya sanar dani yana son gobe da yamma mu fita yawon shakatawa. Wannan bukatar tasa ta zo mini da mamaki, ganin bai taba neman irin wannan bukatar a wajena ba. Nace masa babu damuwa zan nemi izzini a gida.
Ban samu matsala ba ganin shine zai aure ni hakan yasa aka yardar mini mu fita.
Bukatar daya biziro mini da ita ne bayan mun je gidan wani shan kayan sanyi shine ya daure mini kai. Na soma tunanin anya wannan da gaske sona kuwa yake yi ko dai sha'awa ta yake yi. Saboda kirkiri yace mini so yake muyi zina saboda yana cike da sha'awa a yanzu haka. Idan da gaske ina sonsa muje muyi. Cikin mamaki na tambayeshi saurin mai yake tunda gashi mun kusa aure. Nan dai ya nuna bacin ransa daga bisa ya dawo dani gida hakan yasa tun wannan lokacin har yanzun nan ban kara ganinsa ko jin labarin sa ba.
Bayan da iyayena suka dameni da tambaya ne na fito fili na sanar dasu gaskiyar abun da muke ciki. Tun daga wannan lokacin kuma sai auren saurayi ya fice mini a rai. Saboda ina tunanin duk samarin haka suke, sai sunyi lalata da mace kamin su aureta.
Ban jima da Rabuwa da wannan saurayin nawa ba sai kuma ga wani matashi amma shi yana da mata guda, shima ya nuna himma matuka wajen sona da burin na amince masa muyi aure. Bayan nayi dogon nazari ne na bashi damar ya fito. Ya kuma amince cikin kankanin lokaci ya turo ma gabatar sa domin neman izinin iyayena.
Aka kuma amince a bashi, aka sa mana rana nan da watanni shida za a daura mana aure.
Sai dai shima ya sauya mini tunanin na a wani daren daya zo hira gidan mu. Da yake cikin gidan mu yake shigowa hira. Kuma a babban falon gidan mu yasa idan zai fita nake rakashi kofar gida. Gidan mu da akwai zauren daga shi sai kofar gida. Muna zuwa wannan zauren sai naga ya kamoni. Kamun da babu wani na mijin da ya taba mini irinsa a rayuwa ta koda kuwa cikin yan uwa nane. Na biyo shi sai ya haɗa ni jiki na da jikinsa ya soma shafa ta yana kama bakina yana tsotsa. Ni dai ina tsaye gam kamar gunki. A haka har ya biya bukatar sa wajen taba jikinka.
Bayan na koma daki na kwanta nayi ta tunanin ko me yasa yayi hakan. Wata zuciya tace mini sharrin shedan ne na masa uzuri wata zuciyar kuma tace mini shima wannan dan iska ne na rabu dashi. A haka nake dai har barci ya kwashe ni ina cike da wannan tunanin.
Ina tashi da safe sakon dana gani nasa shine ya tabbatar mini da cewa ba sharrin shedan bane, ba kuma kuskure yayi ba na abun da ya aikata jiya. Domin ya nemi da na fito anjima da yamma yana son muje muyi zina saboda tun jiya da yiyi romance ɗina sha'awanta kaiwai yake yi.
Na dauki wayar bayan na natsu na kirashi domin tabbatar da abun da ya turo min. Nan take ya kara tabbatar mini da bukatar sa na son muji muyi zina. Na tunatar dashi lokacin auren mu mai zai sa bazai iya hakura ba. Da kyar dai ya fahimceni yace ya hakura. Sai dai kuma duk lokacin dana rakashi muna zuwa zauren gidan mu sai ya soma romancing ɗina. Ni dai ban taba ɓõye masa ba shi yake kayansa amma kuma bana hana shi.
Akwai wata ranan da ya soma romancing ɗina sai naga yana Ƙoƙarin kwabe mini wando. Nan na zabura mace masa lafiya, ya ce idan har ban amince munyi Zina ba zai fasa aurena. Ni kuwa nace sai dai ya fasa amma bazan iya ba. Abu kamar wasa sai kawai naga ya turo azo gidan mu a karɓi kayan da suka turo ya fasa aurena.
Anan ma iyayena suka nemi jin dalilin sa na yin haka yan aiken suka ce suma basu sani ba. Na kwashe duk yadda muka yi na fadawa mahaifiyarta. Nan take kuwa ta sami mini albarka ta kuma bani hakuri tare da mini fatan samun miji na gari.
Bayan na zauna sauwon watanni takwas bana kula kowa, sai kwasam wani dattijo da muka hadu a asibiti naje dubiya ya nuna yana sona da aure. Ban dai amsa masa ba amma na bashi lamba ta, muka ci gaba da gaisawa yana ta neman umurni ya zo gidanmu mu gaisa. Bayan kamar watanni biyu tsakanin mu sai dai waya na amince ya zo. Na masa kwatance ya zo.
Zai kai sa'an mahaifinmu. Kimanin shekaru 50 zuwa 55. Babu alamun wasa cikin al'amuransa. Ya kuma fadamini yana da mata biyu nice zan zama ta uku idan na amince na aureshi. Kuma zai kaini garin da yafi yin harkokin sa ne na zauna acan ganin bai da mata acan. Nace masa zan yi tunanin zan sanar dashi.
Bayan nayi shawara da mahaifiyarta ne na amince masa da zan aure shi. Ba tare da bata lokaci ba ya turo duk abunda ake bukata na aure. Aka kawo gidan mu bayan da mahaifina ya kara bincike akansa. Kuma yace nan da watanni biyu yake son a daura auren saboda zai yi wata tafiya zuwa kasashen waje sai ya dawo. Muka amince. Daga lokacin ya ci gaba da kula dani tamkar matarsa. Duk kuwa da abunda ya rake shine ya bada kudin sadãki wanda yace sai ranar da za a daura auren zai bayar.
Ana sauran kwanaki 7 yayi tafiya ne ya turo direbansa ya sauke ni, ganin daman munyi alkawari idan yazo zai bani wasu kudi domin na karasa sayayyan auren mu. Naje na sameshi a hotel din da yake sauka idan ya zo kuma yake ganawa da mutane. Duk da na sameshi da mutane ya katsai ya sameni ya mini izzini na shiga dakin kwanan sa zai sameni. Na shiga cikin mintuna goma da shiga ta sai gashi yazo da kudi a Leda miliyan biyu kamar yadda muka yi. Ya mika mini su yace zai koma wajen mutane dereba na jirana ya kaini inda zani. Bayan sallama da muka yi sai naga ya jawoni ya sumbaceni cikin kunnuwa na yake ce mini "kamin nayi tafiya ina son ki amince mini naji dãɗi dake, ma'ana ina son na sadu dake". Ban ce masa komai ba nayi murmushi nace masa sai mun dawo.
Ana gobe zai yi tafiya ne ya nemi nazo hotel dinsa na biya masa wannan bukatar da ya nema. Idan kuwa naki zuwa wannan yana nuni da cewa bada gaske nake sonshi ba. Tamkar nace ya nemi wata ne ya fasa aurena.
Wannan maganar tashi gaskiya ta sakani cikin rudani. A gaskiya ina sonshi ko ba domin kudin sa da yadda yake kula dani ba. Haka kuma na gaji da zuwa da magana daya akan fasa auren da nake yi da maza. Gashi kuma ni kaina ina son naga nayi auren. Gashi sauran watanni muyi auren idan kuma nayi zina dashi sai nayi istibira'i kamar yadda addini ya umurta. Gashi har ga Allah bana so na zina kuma bana son wannan karon ban yi aure ba. Ku bani shawara idan kune wani mataki zaku dauka?
Karin bayani. Masu karatu Wannan shine labarin data turo mana domin neman shawaran mu. Duk kuwa da ta riga ta samu mafita amma dai tana son jin sha'awaran da mutane zasu bata ne domin wasu da suka tsinci kansu a irin wannan yanayi suyi amfani da su.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C