Takaitaccen Tarihin Sarauniyar Kyau Maryam Yahaya

Maryam Yahaya na daya daga cikin fitattun jarumai mata ma su fadakar da mutane a Kannywood.
An haifi Maryam Yahaya a 17 ga watan Yuli 1997 daga zuri'ar Malam Yahaya Yusuf da mahaifiyarta Maimunatu Umar a unguwar Goron Dutse ta nan birnin Kano.
A yanzu tana da shekara 23 daidai.
Maryam Yahaya ta yi karatun primary school a Yelwa inda ta ci gaba zuwa sakandaren Bokabo Barracks.
Ta yi karatun islamiyya a Goron Dutse in da ta ringa zuwa ta daya a alqur'ani da fiqihu. Yarinya ce mai addini da kuma kame kai daidai gwargwado.
Ta na jin yarika uku; Hausa, Larabci da Turanci.
Maryam dai har zuwa yanzu ba ta da aure kuma ba wani mutum da ta shirya nema ko aura.
Maryam Yahaya ta yi shura ne bayan fitowarta a fim din Mansoor wanda ya fito a 2017, duk da ta yi fina-finai da yawa kafin Mansoor.
Ta yi fina-finai da yawa kamar Gidan Abinci, Barauniya, Tabo, Hafeez, Sareena, Mariya, Jummai ko Larai, Hafiz, Gurguwa, Mujadala, Mijin Yarinya da kuma Sareenah.
Ita dai Maryam Yahaya mai kudi ce a yanzu saboda Allah ya rufa mata asiri in da har tana da shagon kayan takalma da sauransu. 

Comments

  1. Ina mai bata shawara data zamo mai rikon addini tasa aure aranta domin shine tsirarta

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C