Shugaban NDDC: 'Abin da muka gano a badaƙalar Hukumar Naija Delta'

Zaman kwamitin majalisar wakilan Najeriya ya yi ranar Litinin a Abuja ya haifar da wasu abubuwan da suka ja hankulan ƴan Najeriya, musamman ma yadda shugaban hukumar raya yankin Naija Delta, NDDC Farfesa Daniel Pondei ya riƙa suma yayin da yake amsa tambayoyi daga ƴan majalisar.
Amma akwai batutuwan da abin da ya auku a zaman kwamitin ya kusa binnewa - kamar ainihin dalilan da suka sa majalisar ke bincikar hukumar ta NDDC da abubuwan da ta gano kawo yanzu.
An kuma jima ana kai ruwa rana tsakanin ƴan kwamitin da kuma Godswill Akpabio wanda shi ne ministan da ke kula da ma'aikatar raya yankin Naija Delta.
Kabiru Alhasan Rurum na cikin ƴan kwamitin, kuma ya yi wa BBC bayani kan abin da bincikensu ya gano.
Cikin abubuwan da kwamitin ya gano, akwai "bayanai da muka samu daga ofishin babban akawu na ƙasa da kuma babban bankin Najeriya waɗanda dukkansu sun kawo bayanai a rubuce na yadda suka saki kuɗade ga wannan ɓangare".
Ya kuma bayyana cewa bayanan sun sanar da kwamitin yadda hukumar NDDC ta salawantar da maƙudan kudaden da aka ware domin ayyukan raya yankin na Naija Delta:
"A bayanan da shugabannin hukumar suka gabatar gaban kwamitin majalisa, sun kama kansu, na farko dai sun ce sun kashe Naira biliyan 81.5 - kuma kowa ya san halin da ake ciki a ƙasar nan da ma sauran duniya. Babu wata ma'aikata da ta gudanar da wasu ayyuka na a-zo-a-gani."
Ya ce tabbas ƴan Najeriya za suyi mamaki su ji cewa an kashe irin waɗannan kuɗaɗe. 
A kan batun halin da shugaban riko na hukumar ta NDDC ya shiga mai kama da suma, ɗan majalisa Rurum ya ce an wa shugaban NDDCn tambayoyi fiye da goma gabanin ya fara suma.
"An yi masa tambayoyi kamar 11, kuma bai iya amsa ko da ɗaya ba cikinsu, kuma shi yasa mu kayi wannan zaman kai tsaye har muka kira gidajen talabijin sun nuna wannan zama namu na wajen sa'a shida," inji ɗan majalisar.
Ya kuma ce wasu da ke cikin ɗakin taron na ganin ciwon da shugaban NDDCn ya ce ya kama shi na gaske ne, amma wasunsu na ganin shiri ne kawai domin ya kauce amsa tambayoyin da ake ma sa.
Bayan da aka fice da shugaban hukumar domin a duba lafiyarsa, shugaban majalisar ya sanar cewa ba za neme shi ya dawo ya ci gaba da amasa tambayoyin ƴan kwamitin ba.
Ɗan majalisa Rurum ya ce wannan bai zama matsala ba, domin gabanin matsalar da ta faru, sun karbi bayanai a rubuce daga bangaren hukumar. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C