Samari Ga Matakan Tinkaran Budurwa A Haduwarku Na farko

Sakamon wasiku da sakonnin tex dana ke yawaita samu ne daga wajen samari musamman wadanda basu taba aure ba na neman yadda zasu tinkari mace da soyayya saboda kunya, tsoro ko shakkun wulakanci da akasarin maza suke dashi ga budurwa a loakcin da suka ganta suke kasa son tinkararta, naga ya dace na fito da wasu dabaru da samari zasu iya amfani dasu domin tinkaran budurwa ko wacce irice a haduwarku na farko. zamu fado sune domin karya kofi da kwarjinin da wasu matan suke yiwa samari masu neman aure.
Abunda ya kamata saurayin da yake son budurwa da aure kuma yake tsoron mata magana ya sani shine, a soyayya kalmomi uku ne mata suke amfani dasu a farkon haduwarta da saurayi.
Kalma ta faro ita ce "e" ta amince, ta biyu kuwa ita ce "a'a" wance samari ke gudunta, ta ukun bata wuce "zan yi shawara". Dukkanin wadannan amsoshin wajen budurwa, basu zama sune hakikanin abunda ke ranta a lokacin data furta maka su ba, don haka kada su karfafa ma gwaiwa kuma kada su kashe ma gwaiwa.
Sai dai kamin nan, ya kamata samari da suke neman matan da zasu aura suma fahimci inane ya kamata su samu matan. "yan mata dai gasu nan a ko ina, sai dai kuma ga namiji mai son aure yana da zabin inda yake son samun matarsa. Wani yafi son iyaye su zaba masa, wani ya nema da kansa, a duk inda kaci karo da budurwar da ka gani kuma kana so amma
shakku da tsoron wulakanci ya bijiroma a zuciya, to ga matakan da zaka bi domin tinkararta, kuma ka shawo kanta cikin sauki.
1; Matakin farko ga duk wani saurayin daya ga budurwa yana sonta, ya natsu ya kalleta da kyau domin nazarin yanayinta, mai alamun saukin
kai ce da ita ko kuwa tanada jan aji. Wannan shine zai baka damar sanin hikimar da zaka tinkareta dashi musamman idan farkon haduwarku kenan. kuma zaka iya fahimta mace wani lokacin ta hada ido da ita,
kayi kokarin hada idanuwa da ita tare da yi mata fara'a ba kuma tare da ta iya fahimta kai tsaye kayi hakan ne domin kana sonta ba.
2; Mataki na gaba shine bayan ka gama karantarta, idan ka tashi tinkararta ka cire duk wani shakku tsoro a ranka ka tinkareta kai
tsaye. Domin mata suna son ganin namiji mai karfin hali da jarumta.
Kuma idan kana gudun wulakacin ne kuma bakaso wani ya gani musamman wanda yasanka, kana iya zuwa kai daya, idan tayi kyau sai ka jawo abokai su ganta.
3; Kamin ka tinkari budurwa a haduwar farko, dole ne ya zamanto kayi shiga mai kyau, wanda zai burge jama'a koda ba ita ba. Kuma ka kula da irin shigar da zaka yi, domin yanayin shigarka yanayin kallo ko fassarar da budurwar zata maka. Mace mai mutunci babu yadda zata kula ka idan taga kayi shiga irin na swagga ko niga. Ita kuwa 'yar birni so take taga kayi shiga irin na samarin birni ba 'yan kauye ba. Kuma idan budurwar mai riko da addini ce, to fa dole sai ka siffatu da addini a shigarka kamin ta baka dama. Don haka shiga wani mataki ne mai
mahimmanci a lokacin da saurayin zai tinkari budurwa a haduwarsu na farko.
4; Baya ga shiga ta kamala budurwa tana son ganin a haduwar farko da sauri saurayin yana da siffa mai kyau. Ma'ana bashi da wata na kasa a tare dashi na halitta muddin shi ne zai tinkareta. Don haka ya kasance idan zaka tinkareta kuma kanada wata na kasa to ka bari sai idan ita kadaice a inda take domin hakan zai bata daman sakin jiki da kai.
5; Kalmarka ta farko ta zamto kalmace ta zuga budurwar da ka fuskata domin zuga yana daya daga hanyoyn shawo kan mace koma wace iri ce. Da wannan ne zata baka hankainta domin sauraron abunda kazo dashi.
6: Wani lakanin jawo hankalin budurwa a haduwarku na farko shine jan wanda take tare dashi kusa da kai ta hanyar yi masa kyauta. Akasarin 'yan mata masu tarbiya basu cika fita ba tare da kannensu ba ko 'yan rakiya, domin saurin jawo hankalinta jawo wanda suke tare da ita zata baka lokacin yi mata magana.
7: Ko samari nawa ne suke da masaniyar cewa mata suna son maza masu barkonci? Jawo hankainta da wani abunda zai sata dariya a haduwarku na farko ko da kuwa haushin kare ne zaka mata. Da farko zata maka kallon samar amma tana baka lokaci zata fahimci kayi hakan ne domin saokanta.
8: Bajinta yana saurin sa ka shawo kan budurwa a haduwarku na farko. Kada ka zama mai rowa, matsolo ko marowaci a haduwarku na farko da budurwa. Kada ka sake ka nuna mata kasawarka ta kowani bangare a haduwarku na farko. Ta dauka cewa bakasan ciwon abun hannunka ba wannan zai jawo hankalinta har ka samu shiga zuciyarta. Dominn ita mace ta tsani namiji marowaci koda kuwa ita ma marowaciyarce.
9; Kada ka sake ka nuwa da kuka yi haduwarku na farko kana da kauyanci ko kunyar shiga mutane ko da kuwa 'yar kauyece ita. Ita mace tana son yin alfahari da saurayi wayeyye kuma dan zamani.
10; Ko kanada masaniyar cewa wasu matan sai kunyi fada kake iya samu kansu? Da akwai wasu matan hanya mafi saukI da zasu saurareka shi ne ka samu sanadiyar tsokanansu, ka tunzurasu har yadda ransu zai baci. Kawai abunda zaka yi kada ka bar wajen har sai ka samu lambar wayarta ko adereshin gidansu. Domin neman sulhu da bada hakuri daga nan zaku shirya kuma ka samu kanta.
Allah Ya bada sa'a. Allah Ya bada zaman lafiya. Kada a manta da gayyatarmu buki idan an dace. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C