Hanyoyin Da Za Ku Kare Muhallanku Daga Ambaliyan Ruwa

Ambaliyar ruwa ibtila'i ne da ake yawan fuskanta a yankunan karkara da birane a Najeriya, wadda ke shafar rayuwar dubban mutane.

A duk lokacin da aka samu ruwan sama mai karfn gaske, akan samu asarar rayuka da dukiyoyi ko cunkoson ababen hawa da fargabar rushewar gine-gine.

Mutanen da suka fuskanci wannan ibtila'i tamkar an tilasta musu rasa matsugunnai ne da dukiyoyi da neman wurin mafaka.

Sai dai masana na cewa ana iya kare ambaliyar ruwa idan aka yi tsare-tsare masu inganci musamman a yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya.Wadanan wasu iyalai ne da suka rasa matsugunni sakamakon ambaliyar ruwa

Farfesa Tanko ya ce, samar da magudanar ruwa hanya ce da za ta rage yawan ambaliyar da ake samu musamman a birane.

''Yawanci a kasashen Afirka ba a mayar da hankali kan magudanar ruwa a cikin unguwani ko kuma a samar da 'yar tsukuku a jikin gida wadda babu wuya ta toshe.

''A wasu lokutan kuma ba a samar da magudanar, kuma shi ruwa idan ka tsare masa hanya zai nemo hanyar sa, '' in ji Farfesa Tanko.

Ya ce wajibi ne a mayar da hankali wajen ganin an gina magudanar ruwa domin sama wa ruwa hanyarsa.BBC ta yi nazari kan yadda za ku iya kare muhallanku daga ambaliyar ruwa, a daidai lokacin da damuna take kara kankama.

A cewar masana wasu matsaloli ne - da a mafi yawan lokaci dan adam ke haifar - ke janyo ambaliya.

A cewar Farfesa Abdullahi Tanko masanin muhalli da ke koyarwa a jami'ar Bayero a Kano, ambaliyar ruwa na faruwa ne duk lokacin da aka samun tsaikon ruwan da ke gudana musamman a lokutan damuna.

Ga dai wasu hanyoyin da ya ce za su iya taimaka wajen kare muhallan ku.

Wannan layi neMadatsar ruwa'
Akasari yankunan da ke dab da kogi na fuskantar ambaliya ne saboda rashin fitar da hanyar wucewar ruwa.

Don haka idan aka samu hanyar da ruwa ke gudana misali kogi ko rafi kuma a ce akwai mutane ko garuruwa da ke rayuwa a kusa da wannan wuri to akwai matsala.

"Wannan yanayi yana kawo ambaliya don haka akwai bukatar samar da madatsar ruwa a irin wadanan yankunan, saboda ita kadai ce ke taimakawa wajen kare ambaliyar ruwa," in ji Farfesa Tanko.Kwashe shara'
Kwashe shara na da muhimmanci sosai, sannan kawai bukatar rungumar al'adar zubar da shara a inda ya dace ba wai watsar da shara a kan tintuna ba, inji masanin.

Ya ce ''daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta shi ne yadda mutane ba su da da'ar zubar da shara yadda ya kamata.

''A unguwanni da dama za ka iske mutane na zubar da shara ba tare da lakari da cewa inda suke zuba sharar hanyar ruwa ba ce .

''Tsaftace magudanar ruwa ba ya yiwuwa sai da kwashe shara. Ya kasance babu datti da ke toshe magudanar ruwa.''

Akasari ledoji na taka rawa sosai wajen tsohe hanyar wucewar ruwa.''Shuke-shuke'
Shukoki na matukar taimakawa wajen kawo saukin ambaliyar ruwa, saboda suna rike kasa duk inda ruwa ke kwararowa suna taimakawa wajen rage karfin ruwan da ke sauka.

Karfin ruwa a kasa musamman a idan babu bishiya ko tsirai na haddasa zaftarewar kasa, kuma idan ana samun wannan yanayi yau da gobe tabbas za a samu ambaliya.

Farfesa Tanko ya ce shuka na da muhimmanci domin tana rage karfin saukar ruwa da gudanar sa, musamman a wurin tuddai.Dumamar yanayi'
An alakanta karuwar ruwan sama a hasashen da hukumar kula da yanayi ta Najeriya ke yi da sauyin yanayin da ake samu.


Wannan na daya daga cikin jigon matsalolin ambaliyar ruwa, kasashen sun jima suna nazari da bijiro da hanyoyin kare muhallansu.

Kasashe da yawa da yanzu ke zama bakin-teku na cikin barazana saboda ruwan teku na karuwwa a kullum, don haka idan an samu mamakon ruwa dole a fuskanci ambaliya.

Source @ BBC HAUSA. 

Masana na cewa akwai bukatar sake jajircewa da fito da tsare-tsaren da za su taimaka wajen rage illolin dumamar yanayi domin ba aiki ne na mutum guda ba.Karin bayani.

A kowacce shekara hukumomin kulda yanayi na hasashen yadda damuna za ta kasance, da yawan ruwan da ake sa ran samu gami da yankunan da ake sa ran samun amabliyar.

Su ma masana kan yi gargadi kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa da jan hankalin mutane kan matakan kare muhallansu.

A bana ma dai akwai hasashen cewa a jihohi da dama na Nijeriya za a iya fuskantar matsalar ambaliyar ruwa, sanadiyyar ruwan sama da kuma cika da batsewar koguna da tafkuna, inda tuni ma wasu yankunan suka fara fama da ambaliyar.

A Najeriya da ke da yawan al'umma sama da miliyan 186 a kullum ana fargabar karuwar al'ummarta da kuma rashin tsare-tsare masu inganci da zasu kare unguwannin birane.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C