Domin Ma'aurata Kaɗai_Yadda Ainihin Farjin Mace Yake

Ba duk maza bane suke da fahimtar cewa kamar yadda halittar azzakarinsu suke mabambamta haka suma mata farjin su yake. Wannan rashin fahimtar kuma bawai ya tsaya bane akan mazan kadai ba. Hatta matan da suke dauke da wannan halittar wasunsu basusan cewa suna da bambamcin farji ba.
Mafi yawan maza sun tafi ne da tunani ko da fahimta koma ta tabbacin cewa, ramin gaban mace ta inda azzakari ke shiga nan ne farjin jima'i mace. Wannan fahimtar kashi 60 na maza suna ɗauke dashi.
Hakan ne kuma yasa sau tari wasu mazan idan zasu kwana suna saduwa da matansu bafa zasu iya gamsar dasu ba.
Dumɓaru, beli wanda aka fi saninsa da suna ɗantsaka. Shine ainihin farjin mace a jima'ince. Kuma shi wannan halittan dake jikin mata ya bambamta ne daga mace zuwa mace. Wasu matan nasu yana da kankanta matuka, wasu kuma yanada girma akwai kuma masu madaidaicin halitta. Wannan halittan da ake samunsa daga saman gaban mace. Yafi ko ina jijihoyi a jikin mace.
Shi dai belin mace bai da wani amfani a jikin mace illa kawai ya jiyar da ita dãɗi a lokacin jima'i. Amfaninsa kenan ba kamar sauran abubuwan da suke kunshe a gaban mace ba.
A zamanin baya kabilu da mutane daban daban sukan ragewa mace tsayin wannan halittan a lokacin da aka haife ta, wanda har yanzu ana samun wasu da suke yiwa 'ya' yansu mata.
A lokacin da sha'awar mace ya motsa, wannan halittan nata jini ne ke kwararowa wajensa. Shi kuma nan take yake kumbura ya kara tsawo yana motsi yadda dai azzakarin namiji yake yi a lokacin da sha'awarsa ta motsa.
Ana samun wasu matan da tsawon dantsakan nasu yana kaiwa kusan centimeters 12, ana iya ganinsa karara kamar azzakari.
Kamar yadda nayi bayani a baya, kowace mace da yadda nata yake wajen tsawo da kuma faɗi dama launinsa.
A lokacinda jini ya kwarara ya kuma kumburo, ya kara tsawo, hakan ne yake baiwa azzakari damar gogansa a lokacin da yake shiga da fita a cikin ramin gaban mace. Wannan gogayyar da yake yi shine kuma yake sawa mace taji dãɗin jima'i har ma ta samu gamsuwa. Don haka ga matan da nasu ke da tsawo, suna iya yin zuwan kai da wuri fiye kuma sa sau guda kamin namiji yayi guda daya. Wasu matan ma tun a lokacin wasa dashi suke samun gamsuwa.
Hakan kuma yasa matan da nasu yake da kankanta suke daukan lokacinsu suna jima'i basu kawo da wuri ba. Duk kuwa da cewa wasu likitocin jima'i sunce tsawon sa da rashin tsawon nasa ba matsala bane.
Ga matan da suke da kankantar dumbaru kuwa sune matan da za a iya kwana akansu ana jima'i dasu basu ma san abunda ake yi ba. Domin basa gajiya, basa kawowa kuma basa jin dãɗin jima'i.
Sai dai bincike ya tabbatar da cewa, kashi 70 zuwa 80 na mata sun fi bukatar ayi musu wasa da dantsaka su da hannu. Wato direct stimulation, wanda cikin ƙaramin lokaci yake sa mace saurin zuwan kai.
Duk da dai bazan kawo cikenken bayani akan yanayin halittar belin mata ba saboda nasa mafi yawan masu karatu suna da kasalar karatu, sai dai yanzu da wannan dan bayanin maza dama matan sun fahimci shi ramin gaban mace amfaninsa a lokacin jima'i shine hanyar da maniyi zai bi ya shiga mahaifa amma ba shi bane yake samar da jin dãɗin da mace ke samu ba a lokacin saduwa da ita. Hatta ruwan dake fita daga gaban mace daga jikin dantsakanta yake fita saboda amfaninsa kawai kenan ya jiyar da mace dãɗin jima'i. Shi kuma Namiji shigar da azzakarinsa cikin ramin ke Samar masa da jin dãɗin da zai yi zuwan kan da maniyi zai fito ya shiga mahaifa.
Don haka girman ramin gaban mace bashi bane girman farjinta. Shi girman ramin gaban mace yana iya canzawa idan tana so a kuma duk lokacin datake so a kuma yadda take so. Amma dumbarunta ba zai taba canzawa ba sai dai ko a yanke shi ko kuma a masa aikin tiyata a kara masa tsawo ko fadi.
Wannan yasa maza masu basira suke yiwa matansu wasa sosai ta hanyar sotsan farjin su da kuma musu wasa da dantsakansu da hannu.
Wannan ne kuma yasa maza ke mamaki idan sunga duk da irin yadda suke saduwa da matansu amma kuma suna yin Madigo. Saboda shi maɗugo kai tsaye ake murzamata kan dantsakanta kuma a sha mata shi wanda nan take yake sa ta samu biyan bukata ba kamar yadda mijin nata shi zai durfafi zura azzakarinsa ne a ramin gabanta da sunan yana biya mata bukata.
Wannan shine hakikanin bayani a takaice akan farjin mace da kuma ramin gabanta.
Idan da mai neman karin bayani ko tambaya a sarari ko a ɓõye yana iya yi. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C