Babban Bankin Najeriya CBN Ta Haramta Shigo Da Masara Cikin Kasar

Babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci duk dillalai masu izini da su daina safarar masara zuwa cikin kasar.
Babban bankin na CBN ya sanar da hakan ne a wani daftari da Dakta Ozoemena Nnaji ya sanyawa hannu, wanda shine Daraktan Kasuwanci da musaya a sashin bankin dake Abuja.
Haka zalika Babban Bankin ya umarci dukkan dillalan da suka samu izini a hukumance da su gabatar da jerin nau’in Masarar da aka riga aka yiwa rijistar dan Shigo dasu Cikin kasar.
Babban bankin ya umarci dillalan da abin ya shafa da su yi hakan a gabanin rufe kasuwancin a ranar Laraba.
Ya yi bayanin cewa matakin wani bangare ne na kokarin da CBN ya yi na kara samar da kayayyakin cikin gida da kuma farfado da tattalin arzikin kasar cikin sauri. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C