Yanzu Ne Annobar Covid-19 Za Ta Fara Ɓarna A Najeriya –Gwamnatin Tarayya

Yanzu Ne Annobar Covid-19 Za Ta Fara Ɓarna A Najeriya –Gwamnatin Tarayya
Kwamitin Shugaban Ƙasa na yaƙi da Covid-19 ya bayyana cewa da alama yanzu ne za a fara ganin tasirin wannan cutar a najeriya.
An bayyana hakan ne lokacin da ‘yan kwamitin suka bayyana a gaban kwamitin haɗin guiwa na Majalisar Wakilai don bayar da bayanai kan maƙudan kuɗaɗen da aka warewa kwamitin da kuma waɗanda aka kawo na gudunmuwa don yaƙi da wannan cuta.
Kwamitin yaƙi da cutar ta coronavirus ya nuna damuwarsa kan yadda ‘yan Najeriya su ke ƙin zuwa a yi musu gwaji, wanda a cewarsu hakan ne dalilin da ya sa ake samun ƙarancin yawan mutanen da aka yi wa gwajin cutar a cikin al’umma.

Jaridar Punch ta ruwaito Shugaban kwamitin yaƙi da koronar, wato Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, yana cewa akwai rashin tabbas a al’amarin annobar, inda ya yi kira da ‘yan majalisar don su taimaka wajen isar da saƙon wayar da kai ga al’ummomin yankunansu.
Ya ce, “Ya zama dole in faɗi cewa har yanzu cutar tana da matukar hatsari. Ba mu kai maƙura ba; sai mun yi kyakkyawan shiri. Babu wani ƙayyadadden lokaci; shi ya sa ma ba a kashe kudi ba saboda sai yanzu ne aka saki kuɗin.
“Babu wani magani ko rigakafi ga wannan cuta. Cutar ta sha kan duniya baki ɗaya. Duk abubuwa sun hargitse. A yau ga shi duk mun rufe hanci da bakunanmu. Ba mu taɓa fuskantar irin wannan ba.”

Da kuma aka tambayi Shugaban Hukumar Yaƙi da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu, cewa ko kwamitin yaƙi da cutar ya ƙiyasta adadin yawan da cutar za ta kai maƙura a Najeriya, sai ya ce ai yanzu ne ma cutar ta fara yaɗuwa.
“Har yanzu muna tsakiyar annoba mai matuƙar hatsari. A gaskiya ma, akwai alamun cewa har yanzu muna farkon annobar ne. Wannan ita ce haƙiƙar gaskiya.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C