Yadda Ake Tarairayar Mai Ciki Domin Dan Cikinta

Jama’a barkanmu da sake saduwa cikin filinmu mai albarka, na Taskira yau za mu tabo batun Raino kafin ita tarbiyyar, raino sh ima zaman kansa yake tun daga samuwar ciki har zuwa sanda Allah zai sauke mace lafiya tana tattare da tattali, wahala, da ciwuka, saboda daukan ciki ba’abune mai sauki ba.
Tun daga daukansa mata sukan shiga cikin na’ui iri iri fari da baki saboda ita mace ta kasu kashi kashi akwai matan da ba ruwansu da laulayi ko tsarabe tsaraben ciwuka, ko kwadayin son abu kaza kin abu kaza wata ma sam bata jin kamshi, wari ko wani abu, wanda ta wani fannin akwai mata masu jin wadannan abubuwan.
Wani cikin baison cin komai na dangin abinci, wani kuma mace zatayi ta ciye ciyenta tamkar ma bata da matsala, wata ko wari take son shaka wata kuma ruwan famfo ko na roba ba ta so sai ruwan rijiya, tsarabe tsaraben ciki nasa mata da dama cikin ha’u’la’i saboda wani ma namijin baya gane mai matarsa ke ciki balle ya san ta yarda zai taimaka mata, wani kuma ya sani amma tsabar kar ya yi sai ya ce ta cika fitina da son kashe kudi, wanda hakan na iya jawowa mai ciki ta zamo cikin kasala da bacin rai, wanda wannan na da matukar wahala da hatsari ga mace mai juna biyu, yana da kyau maza su kula da matansu yayin samuwar cikinsu, su nuna musu soyayya da tarairaya yadda mace za ta kasance cikin farin ciki da annushuwa da ingantar lafiyarta da ta jaririnta, addabar takaici nasa mace samun matsala gun haihuwa saboda ita mace mai ciki ana son ta kasance cikin farin ciki da wslwala zai iya shafar abun cikinta ya kasance cikin sukuni shi ma da girma, amma muddin ana yawan samun sabani tun da na ciki na shafar rayuwar yaron wanda ba lallai ne a gane ba sai a danganta mace da ta cika korafi, son a kashe kudi ko iya yi sai ya kasance mace na ramewa jininta na kasa, zuciyarta ba wala wala, ta fara rama, ko ciwo yafara mata sallama, ta rasa kwanciyar rai sai hakan ya shafi lafiyarta data jaririnta, amma in yakasance kuwa tana samun abunda takeso to da ita da jaririnta suna cikin farinciki Sai haihuwa tazo wa mace da sauki batare da wani barazanar ciwo ba, yawancin abinci mai kyau da lafiya na matukar kuzari ga mai ciki Ana bukatar mace mai ciki ta kasance cikin Tsafta Ana nufin tsaftar jiki, kaya, muhalli, abinci, abinsha, bandaki wadannan yana da kyau duk mace mai ciki ta kiyaye domin dan jikin ki na bukatarsu Farin ciki Ana nufin mace mai ciki ta kasance cikin walwala, sa farinciki, zama da mutanen da za su sata farin ciki, kadaice bacin rai tana iya yin duk yadda za a yi ta zama cikin fara’a domin yanayinki yanayin Danki Cima Ana nufun mace ta kiyaye irin abincin da za ta ci, don inganta lafiyarta da ta danta.
Kayan marmari irinsu:
Data, lemo, kwakwa, ayaba, salad, zogale, kwai, wake da sauransu Ababan debe kewa Ba a son mace mai ciki ta zauna ba fara’a ko saka damuwa a ranta anfisin ta yi abubuwan da za su sa ta farin ciki kamar Kallo, karatu, motsa jiki, da sauransu.
Abubuwanda ba a so mace mai ciki ta kasance a ciki Yawan damuwa, yawan sa bacin rai a rai, kuka, fada, rashin hakuri, zama ba motsa jiki, yawan korafi wadannan iloli ne marasa dadi ga mace mai ciki yana da kyau ta kiyaye su ta zamo mai tattalin kanta da abun jikinta ko inganta wa kanta rayuwa mai dadi.
Tarbiyyar da na farowa tun daga Reno saboda haka mata su kiyaye wadannan abubuwan yayin da suke da ciki idan Allah ya nuna mana sati na gaba za mu dora a kan mazaje da abubuwan da za su rinka taimaka wa matansu yayin rainon ciki, har zuwan yaransu duniya, yakin tarbiyya ba na mace ne daya ba har da ku mazaje domin ku ne kashin gida, ba wai a sakar wa mace ragamar gida ba dole sai namiji na tallafawa. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C