Sirrin Zaman Aure Na Gari

Kama daga neman auren zuwa bukukuwan da ake gudanarwa na auren ana yinsu ne cikin farin ciki da kuma annashuwa tattare da 'yan uwa da abokan arzikin wadanda auren ya shafa. Haka kuma duk ma'auratan da suka yi aure a matsayin mata da miji burinsu suga cewe mutuwa kadai zai iya rabasu.
Sai dai kuma duk da wannan fatan da ma'aurata suke dashi game da zaman
auren nasu, zaki ga cewa macecen auratayya ya yawaita a wannan lokacin namu wanda kuma hakan yana jawowa sha'awar auren wajen wadanda basu yi ba rashin sha'awar yin auren.
Ga ma'aurata mata da mazan da suka yi sa'a suka samu kansu cikin ma'aurata, to ya zama tabbas suyi kokarin gano da kuma neman sirrin
illimin zaman aure da abokan zamansu domin samun zaman auratayya na gari. Haka kuma rashin sanin wannan da kuma rashin maida hankalin wajen neman sanin yasa maza da mata da dama a wannan lokacin suka kasa
hakuri a zaman aurensu.
Shi daia zaman aure zamane da wadanda suka yi zasu dauka kuma su kudura a ransu cewa sunyi wannan auren ne domin rufawa junansu asiri da kuma taimakawa juna ta bangarori da hanyoyi da damar gaske, haka kuma babu zaman dayake bukatar hakuri ga masu yinsa irin zaman aure ga ma'aurata.
Sau tari matsalar zaman auren da ma'aurata suke fiskanta ya samo asaline tun daga lokacin da suke neman auren, domin wasu ma'auratan
maza da mata suka yi kokarin ganin sun shigar da yaudara da kuma karairayi a lokacin da suke gudanar da soyayyarsu na zaman aure.
Wannan dabi'ar ba wai ga maza kawai ta staya ba kamar yadda ake gani, har suma mata cikinsu ana samun wadanda basa fitowa kara su fadawa manemansu gaskiyar asalinsu, ko yanayin gidajensu, wasu matan 'yan talakawa ma har nuna gidan masu kudi a matsayin sune iyayensu da zasu daura masu aure ba tare da fayyacewa maneman nasu gaskiya lamarin dake tsakaninsu da gidan masu kudin ba, wanda hakan daga bisani yakan iya jawo matsala a zaman auren nasu.
Babban matslar da mafiya yawan ma'aurata suke fiskanta a wannan lokacin shine na rashin samun cikenkiyar sadarwa a tsakaninsu domin
shi sadarwa na zaman aure shi ne abu da yake tattare da dukkanin sirrin zaman aure na gari. A ciki ake samu hakuri, ladabi da biyayya
da kuma jurewa zaman aure hade kuma da alkinta romunta da kuma boye sirrin juna da kuma bayyana alherin cikinsa.
Duk da ana ganin cewa kamar yanzu an samu fhimtar wayewa ta zaman takewar aure, har yanzu ana samu wasu ma'auratan da suke zaman uban gida da yaronsa, inda zaki ga cewa mai gida baya sakarwa matarsa fiska
ba yada lokacin hira da ita sai a lokacin da yaje bukatarta, haka nanma da a kawai wasu matan da suka fi karfin mazajensu kodai ta
dukiya ko kuma ta wani matsayi ko mukami, don haka suma basu da lokacin zama da mazan nasu domin tattauna al'amuran da suka shafi zaman auren nasu.
Babban sirrin zaman aure na gari wajen ma'aurata shine ya zama suna da kyankyawan fahimtar juna a duk lokacin da wata matsala da taso a tsakaninsu. A irin wannan yanayin dolene su zauna su zama su tattauna duk wani lamarin daya taso masu musamman ma na matsala.
Rashin kyankyawar sadarwa a tsakanin ma'aurata shine ummal aba'isan matsalar macecen aure. Ga ma'auratan da suke burin ganin sun samu zaman aure na gari a tsakaninsu, dole a kullum ya zamanto suna kokarin fahimtar juna a dukkannin al'amuransu na yau da kullum. I dan mai gida yaga wani lamarin da bai masa kyau ba ko kuma bai fahimta ba, yana da kyau ya nemi bayanin lamarin wajen uwar gida cikin natsuwa da fahimta, haka ma ita uwar gidan.
Manyan matsalolin dake yawan tasowa a tsakanin ma'aurata wanda kuma yake jawo masu sanadiyar rashin jituwa wani lokacin ma harda mutuwar aure sune yadda ma'aurata suke boyewa junansu wasu muhimman al'aumaran da suka kamata su tattauna a tsakaninsu. Misali lamuran da suka shafi
tarbiyan yara, malakan wasu abubuwa na dukiya, kula da dukiya, karrama 'yan uwan juna,karin aure da kuma matsala na kwanciyar jima'i.
Wadannan suna daga cikin manyan abubuwa da akasarin ma'aurata suka kasa sanin yadda zasu tafiyar dasu wanda a sakamakon hakan zaman aure na jin dadi yake gushewa daga garesu.
Sau dayawa wani bangare na ma'aurata na nuna fifiko game da yadda za a tafiyar da tarbiyan yaran da suka haifa, inda zakiga cewa miji zai yanke wani hukunci akan 'ya'yansa ba tare da neman shawaran uwar yaran
ba, haka itama matar tana iya yin hakan ba tare da neman shawara ko izzinin mijin ba, wanda hakan daga bisani na iya haifar da mummunar
rashin jituwa a garesu.
Duk arziki ko matsayin miji ya zama dole a duk lokacin da zai yanke wani hukuncin daya shafi tarbiyar 'ya'yansu ya nemi shawarar matarsa
koda kuwa nata gudumawar da zata bayar ba zaia zama mai tasiri ba, haka ma ita. Domin sau tari akan iya ganin saboda mulki ko matsayin da uba yake da shi a gidansa baya neman shawaran ko na gaba dashi bare
kuma matarsa ta gida, wanda lamari daga bisani na iya cutar da uwar 'ya'yan da aka aikatan hukuncin ba tare da neman shawarar ta ba. Haka wasu matan masu hannu da shuni ko kuma matsayi suma suke gudanar da lamarin gidajensu ba tare da tuntubar mazajensu ba, wanda hakan bayan rashin jituwar da kan iya jawowa a tsakanin ma'auratan, lamarin na iya
zubar masu da mutunci a gaban 'ya'yan nasu da kuma al'umar da suke ciki.
Ma'uarata da damar gaske zaki samesu suna boyewa junansu abubuwan da suka mallaka na dukiya, miji yana boyewa matarsa arzikin dayake dasu a waje, haka itama macen tana boyewa mijinta sana'a ko kuma gidajen data
mallaka idan badasu mijin ya aureta, lamarin da daga bisani idan guda daga cikinsu ya gano yake zama matsla, ko kuma idan daya ya riga guda mutuwa yakan iya zama tashin hankali da kuma hayaniya a wasu lolkuta.
Aure na gari yana bukatar ma'aurata su rika kokarin fahimtar da junansu game da al'aumaransu na yau da kullum, ba shi yiwuwa ma'aurata su boyewa junansu irin sana'ar da suke ciki, abokan mu'amalarsu, mai suka mallaka, suwa suke bi bashi suwa kuma ke binsu. Hakan yana da kyau ne domin ganin kusancin ma'aurata sune ya kamata a soma jin duk wani sirrin dake tsakaninsu ba wai sai an fita waje ana neman bayanin abunda ya kamata a cikin gida a sani ba musamman saboda halin yau da kullum domin babu wanda yasan gawar fari a tsakanin miji da mata.
Musamman ga duk magidancin dayasan yana da mace fiye da guda, to bayyana sirrin abunda ya mallaka ya zamemasa dole ga matansa da kuma makusantarsa. Haka itama macen da Allah yayi mata wadatar dukiya kuma take da kishiyoyi, boye abunda take da shi zai iya zamemata matsala nan gaba, dole ne ta fito fili ta nunawa duniya irin abubuwan data mallaka ba don alfahariba sai domin gudun abunda ka iya zuwa ya dawo.
Irin halain ko na kula da wasu ma'aurata suke nunawa ga dukiyoyin junansu, shima wannan matsalace babba da yake jawo rashin zaman
lafiyar ma'aurata a gidajensu. Wasu mtana basu dauka cewa dukiyan mazajensu dole ne su kula dasu, haka suma mazan da matansu suka fisu abun duniya basu damu da kula da kuma alkinta dukiyar ba.
Ana samu mijin dake daura matarsa akan dukiyar daya mallaka domin ta kula masa dasu, amma kuma daga bisani ta nuna ko oho ga dukiyar ta hanyar rashin kula ko tsawatarwa da duk wani abunda taga na iya zama asara a dukiyan, hakama su mazan da matansu suka daurasu kan dukiyoyinsu.
Yana da kyau ma'aurata su fahimci cewa, shi arziki na Allah Ke badashi, kuma ga wanda yake so, kuma hakkin junansu ne su kula da
dukiyar junansu domin kowanne cikinsu yana da gadon guda bayaga amana da kuma zamantakewar auren dake tsakaninsu da so da kauna. Dole ne macen ta kula da duk wani dukiyar mijinta da aka bata amanar kula
dashi kai tsaye ko kuma a kaikaice, duk inda ta ga cewa a kwai nakasu ga wani shirin da akayi ko akeyi domin kawo barna a cikin dukiyar
mijinta dole ne ta saka baki cikin lamarin domin kawo gyara, haka shima mijin nata ya kamata yayi ga dukiyar matarsa idan hakan ya kama.
Kula da kuma ganin mutunci 'ya'yan uwan juna wani sirri ne dake kara dakon zaman auren ma'aurata. Babu matar da zata rike 'yan uwan mijinta da mutunci ko da kuwa ita suke cutarwa suga bayanta, domin a kullum sai dai su zageta a son rai amma ba da hujja ba, don haka kuma Allah ne zai zama mai kareta daga dukkannin wani kaidin da za a shirya mata
domin rabata da mijinta amma da sharadin idan babu mummunar kulli itama a zuciyarta.
Dole ne mijin ya zama mai mutunta iyaye da kuma 'yan uwara matarsamuddin dai yana neman zaman aurensu ya zama mai garko kuma abundakwatance, haka kuma duk wani makirci da sharrin da matarsa zata shirya
masa a wajen 'yan uwanta babu mai sauraronta ganin yadda yake karramasu da kuma ganin mutuncisu. Babu wata mace ta gari da zata ga mijinta na ganin mutuncin 'yan uwanta da iyayenta ta kasa natsuwa a zaman aurenta don haka ga dukkannin ma'auratan dake fatan ganin su samu zaman aure na gari, to ya zama dole su mutunta 'yan uwan juna da kuma iyayen juna.
A cikin kashi 100 na maza kashi 30 ne kawai suke iya fitowa fili sufadawa matansu suna neman aure kuma zasu kara aure, wanda hakan yake jawowa ma'aurata matsalar da wasu lokutan aure ke mutuwa. Babu shakka
mata da dama suke jawowa mazajensu na boye masu lamarin kara aurensu saboda irin bakar kishin da suke nunawa, amma kuma hakan ga duk wani na mijin dake neman kafa hujja akan matarsa, dole ne ya fito fili ya
fadawa matarsa shirinsa na kara aure da kuma hujjarsa na yin hakan koda kuwa ba zata gamsu ba cikin natsuwa da kwaciyar hankali.
Tabbas duk matar da a yau ta ji daga bakin mijinta cewa zai yi mata kishiya bazata ji dadi ba, amma kuma babu wata matar da zata so ta
wayi gari a ce mata an daura auren mijinta a yau bata samu tabin hankali na wasu 'ya dakikoki ba ko awanni, don haka fadawa mace shirin neman aurenka tun da wuri yafi a fada mata a kurarren lokacin. Ya kuma kamata mata su fahimcicewa a duk lokacin da maza suka kuduri aniyar kara aure, fada da neman tashin hankali baya sa sun sauya ra'ayinsu, a
irin wannan lokacin babu abunda ya kamaci mace illa ladabi da kuma addu'ar fatan alheri ga burin mijin naki idan akwai alheri Allah Ya
tabbatar idan kuma babu ya sauya da abunda ya fi muku alheri. Muddin ma'aurata suka dauki wannan matakin a zamantakewarsu na aure babu wata matsala na tashin hankalin da zai taso musu.
Kwanciyar jima'i yana daya daga cikin abubuwan da suke jawo matsalolin zaman aure, haka kuma yana daga cikin sirrin zaman aure mai dorewa. Dole ne mace ta tabbatar da cewa tana iya biyawa mijinta bukatarsa ta jima’I a kowani lokaci da kuma yanayi. Haka shima na miji ya zama dole ya tabbatar da cewa kamar yadda matarsa take kwantar masa dasha’awarsa shima yayi kokarin ya biya mata tata bukatar na jima’i. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C