Shin Kun San Muhimmancin Ilimi Ga 'Ya 'Ya Mata Kuwa?

Da sunan Allah Mai Rahma Mai jin Kai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka.
Da farko zanyi amfani da wannan kafa tamu ta soshiyal midiya wajan karfafar yan uwana mata akan muhimmancin ilimi. Saboda munsan cewa; ‘shi neman ilimi wajibine akan dukkan Musulmi’ anan zamu ga ba’a ce akan Namiji kadai ba, kema mace wajibine ki tashi ki nemi ilimin addini da na boko.
Ilimi ya na da matukar muhimmanci ga ‘ya mace saboda da ilimi ake tarbiya, ita kuma tarbiya ana samune daga ‘ya mace, to dole mace ta gari ta zama mai ilimi da tarbiya ta yadda zata tarbiyantar da yaranta.
Domin ko Manzon Allah (S) da ya lissafawa maza irin matayan da zasu aure sai da yace, wacce tafi itace ku samu “MA'ABOCIYAR ADDINI” To kunga taya mutum zai zama ma'abocin addini ba tare da ilimi ba?.
Wani Abu da bamu sani ba shi ne, idan aka samu mace ma'abociyar ilimi kuma take kokarin ba da gudummawarta a makaranta ne ko a gida ne, za kaga ana girmamata sosai ko da kuwa karamace a shekaru, saboda munsan cewa shi ilimi na kai mutum ya zamo babba.
Da wannan nake kiran ‘yan uwana mata da mu tashi mu nemi ilimi, Domin Manzon Allah (S) cewa yayi muje mu nemi ilimi ko da a birnin sin ne. Haka ma Sayyada Zahra (as) tace; ‘Neman ilimi farillah ne akan dukkan Musulmi.
Ya ‘Yar uwata ki nemi ilimi ko dan gyara tsakanin ki da mahaliccinki, kisan waye shi, kisan taya zaki bauta masa?
Ina rokon Allah ya bamu ilimi Mai amfani, ya kuma bamu damar neman. Wassalamu Alaikum warahmatullah ta'ala wa barakatihu. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C