Pantami Ya Tattauna Da Turawa Kan Batun Harkar Noman Nageriya

Maigirma Ministan Sadarwa da bunkasa tattalin arzikin Nigeria Dr Isah Ali Ibrahim Pantami yayi tattaunawa da kungiyar tarayya a birnin Brussels daga Nigeria ta hanyar amfani da tattaunar kusa ta na'urar sadarwa (Virtually Conference call ) wato Live chart kenan.
Maigirma Ministan shine ya jagoranci tattaunawar wacce ta danganci inganta fasahar harkokin noma a Nigeria domin samar da cigaban tattalin arzikin Nigeria
Dr Isah Ali Pantami yace yayi magana ne a matsayin hadin gwiwar su na (MIT) na Ma'aikatar da take samar da bunkasa Tattalin arziki da manufofin samar da dabaru akan yanda kungiyar tarayyar tura (EU) zasu nuna goyon bayan su ga Afrika musamman Nigeria akan samar da fasaha
Maigirma Minista Dr Isah Ali Ibrahim Pantami kullum a cikin aiki yake da nazarin hanyoyin da za'a bunkasa tattakin arzikin kasa, tun lokacin da aka fara wanna zaman killace mutane a gida baiyi kasa a gwiwa ba ya samar da fasahar da shugabannin Nigeria zasu dinga tattaunawa akan al'amuran kasa ba tare da an hadu da juna ba domin kada Kasar ta tsaya, a mai'aikatar sadarwa kullum sai cigaba ake samu. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C