NAZARI_Akwai Bambanci Masu Yawa Tsakanin Gwamnonin Arewa Da Na Kudu

Kamar yadda kuke ganin hotunan Ukun farko gwamnan jihar Legas ne Babajide Sanya-Olu lokacin da yaje fadar shugaban ƙasa dan yi masa jawabi akan irin abubuwan da suke wakana na tashin hankali, shi ne ya kwakwashi hotunan wararan da lamarin ya faru domin nunawa shugaba Buhari domin ya ganewa idanun sa tare da bayyana buƙatun mutanan jihar sa da abun da suke buƙata a yankin nasu, YARBAWA KENAN SUN FI ƳAN AREWA IYA SIYASA Musamman siyasar cikin gida sannan suna da biyayya ga sanin girman manyan su duk da cewa basu fiye yin wani ayyuka ba amman suna da haɗin kai da kishin mutane su.
Amman ku dubi sauran hotunan na ƙasan su gwamnonin mu ne na arewa nada dana yanzu wanda suka kakkai ziyara fadar shugaban ƙasa kusan dukkan nin su an samu matsaloli a jihohin tunda kan rashin tsaro da sauran abun da zai taɓa zukatan talakawa, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka da gidaje na dubban mutane wasu kuma an yiyyi gobara da ruwan sama ya share dukiyoyin dubban mutane, amma ba su iya ɗaukar hotunan irin asarar da talakawan da suke mulka suka yi ba domin nunawa shugaba ƙasa Buhari ko hakan zai sa ya fi nutsuwa tare da tsayawa tsayin daka domin gyara wasu abubuwan da suka ɓaci jihohin su.
Magana ta gaskiya shi ne gwamnonin mu na arewa suna ƙoƙari sosai wajan ayyuka da kawo sauye-sauye a wurare daban-daban ko ƴan adawa sun san haka, amma tunani sune ya kamata su fito da irin wannan salon na zuwa da hotunan matsalolin al'ummar su gaban shugaban ƙasa. tunda dai arewa ta jima a cikin matsalar tsaro da mawuyacin talauci ga rashin wuta da tayi sanadiyar rufe dubban kamfanoni hakan yasa mutane rasa aikin yi kuma kowane gwamna daman can shi ne wakilin shugaban ƙasa a jihar sa, wanda akwai mutane iri na da muke zargin cewar ana ɓoyewa shugaban ƙasa wasu abubuwa dake faruwa a matsalolin rashin tsaron da suka addabi wasu daga cikin yankunan arewacin Najeriya, Ya kamata su farka muma muga sauyi hakan a nan gaba duk gwamnan da zai ga shugaban ƙasa ya tafar masa da tilin hotunan irin ci gaban da ya samu dana inda al'umma ke neman a kai musu ɗauki musamman ɓangaren rashin tsaro KAMAR YADDA AKE WATSA HOTUNA A SOSHIYAL MIDIYA Idan wani lamari ya auku Allah Ta'ala ya basu iko gyarawa domin ta irin haka ake barin mu a baya.
A ƙarshe dole fa mu fara ɗora niyya gyara harkokin siyasar mu ta koma ta ci gaba tare da tsara manufofi masu kyau domin kawowa yankin arewa sauyi ingattacce, sannan mu kammu da ake mulka sai mun gyara ta wajan daina zagi da aibata shugabannin mu tare da basu goyon baya akan kowane irin ci gaba idan yazo mu daina saka siyasar ɓangarenci da son rai kowa yasan cewa kaf ɓangarorin Najeriya mu ne ba ma son namu bama kishin na mu kuma mune marasa tsari a kowane fannin rayuwa a fadin ƙasar nan, Allah ya sa mu gane mu gyara domin gaban mu ta yi kyau, Allah Ta'ala ya kawomana ƙarshen duk wata matsala musamman ta tsaro da ta addabi yankin mu na arewa dama sauran sassan jihohin Najeriya duk wanda yake da hannu wajan jefa talakawa cikin matsanancin hali yana sani Allah ya yi mana maganin sa kowaye shi.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C