Najeriya Zata Murmure Farashin Mai Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A Duniya

Babu shakka wannnan labari ne mai dadi ga kasashe irinsu Najeriya da su ka dogara da arzikin mai. A cikin farkon makon nan gangar danyen man Brent ya kai har Dala $40.42 a kasuwar Duniya.
Mai bai taba yin irin wannan tsada a kasuwa ba tun cikin farkon Maris. A ranar Talata 2 ga watan Yuni, 2020, farashin wannan samfari na mai ya kara kudi da fiye da kashi 3.3%, kamar yadda mu ka samu rahotanni daga jaridun kasashen waje.
A daidai wannan lokaci gangar man WTI na kasar Amurka ya kara farashi da kusan 2.0%. Man WTI wanda ake saida gangarsa a kan $37.49 ya tashi zuwa $37.88 a makon nan.
A ranar Talatar ne kuma majalisar tarayyar Najeriya ta taba lissafin da aka yi na abin da ake hasashen kasar za ta samu, hakan bai rasa nasaba da yadda kasuwar ta ke tafiya.
Sanatoci sun yi hasashen cewa za a saida gangar man Najeriya a kan $28 a kasuwar Duniya, akasin fam Dala $25 da shugaba Muhammadu Buhari ya yi lissafi a kwanakin baya.
Kungiyar OPEC ta kasashen da ke fitar da mai a Duniya ta na tunanin cigaba da rage adadin danyen man da ta ke hakowa har zuwa cikin watannin Yuli da Agusta da za a shiga. Rasha da sauran kasashen OPEC ba su hako abin da ya haura ganga miliyan 9.7 duk rana.
Wannan ya na nufin an rage kusan 10% na abin da ake samu a kasuwannin mai.
A cikin watan Afrilu sai da farashin gangan man Brent ya karye zuwa $15. Tun daga lokacin da OPEC ta rage adadin abin da ake hakowa, danyen man ya rika kara daraja. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C