Munanan Illolin Auren Dole a Cikin Al’umma

Wannan matsalace da ta dade malamai da masu sharhi suke ta kwarmato da babatun jawo hankalin iyaye su daina yi wa ‘ya’yansu, domin wannan dabi’ar tana taimakawa matuka wurin ingiza wasu matan ga fadawa yawon duniya ko kuma su gwammaci su kashe mijin da aka ba su ko dai kansu. Da ni, da kai mai karatu, mun sha jin labarai na wadanda suka kashe mijin da aka ba su saboda kiyayyar auren dole da aka yi musu.
Haba iyayenmu mene ne alfanun takura wa ‘ya’yanku a kan dole sai sun yi auren wadanda ba sa kauna? Babban burinku shi ne, yaranku su yi aure su zauna a gidajen mazajensu, ba burinku su fito ku dinga jera kafa da su a cikin gida ba, sannan abun bakin ciki ne gare ku a ce yaranku suna ta kai kawo a layi kwararo-kwararo, lungu-lungu sako-sako saboda ba su da aure.
Kuna sane da cewa auren dole shi ya janyo mana fituntinu da muke ciki saboda illar auren dole kasancewar mun saba wa maganar Manzon Allah.
Ina kira ga iyaye da su yi wa ‘ya’yansu adalci su barsu su auri wadanda suke so don a samu zaman lafiya da zuri’a dayyiba.
Ko iyaye suna sane da cewa saboda wasu iyayen na hana su auren masoyansu hakan kan sa wasu ‘yan matan su bai wa masoyan kansu don aikata alfasha, tun da dai iyaye kun hana su aure ai ba za ku hana su zinace-zinace ba.
Wallahi na taba tsintar wani labari wanda nake da sahihancinsa don ganau ne ni ba jiyau ba hasalima nine na zamo sanadin hana wancan mummunan bada’i da iyaye suke kokarin jefa ‘ya’yansu a ciki.
Labarin shi ne; Wasu masoya ne suke tsananin so da kaunar junansu sai iyayen bangare daya suka jajirce a kan ba za su karya maganar wancan ba, kasancewar wancan aka fara tsayarwa daga baya wannan din ya karkatar mata da hankali ta fada sonsa, saboda Allah ke saka soyayya kuma shi ne ya saka mata soyayyarsa shi ma kuma haka.
Sun yi sun yi abun ya ci tura hakan ya sa yarinyar ta kawo masa shawarar cewa me zaihana ya neme ta (ya sadu da ita) indan ya so dolen iyayen su barta ta aure shi idan suka ga ciki ya bayyana.
Ire-iren hakan ba sa kirguwa sai dai kiyayewar Allah. A karshe ina kira ga ‘yan matan da samari da su ji tsoron Allah su dinga rungumar kaddara idan har irin hakan ta faru.
Su kuma iyaye su ji tsoron Allah su dinga bai wa ‘ya’yansu wadanda suke so, su tuna fa yanda suke jin so haka suma yaransu suke ji. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C