Matakan Karfafa Soyayya Tsakanin Ma'aurata

1.Fifita Aboki/ Abokiyar zama na da muhimmanci wajen sabunta dangantaka, idan an yi aure, soyayya ba ta dorewa har abada amma kada mutum ya kuskura Aboki/ Abokiyar zama ya fita daga cikin abubuwan da za a fifita a rayuwa bayan 'ya'ya, abokai da kuma sana'a. A rika tunatar da Aboki/ Abokiyar zama muhimmancin juna.
2. Ci gaba da dorewar tsarin kwalliya a bisa yadda aka fara gina dangantakar. Zaman dindindin ba lasisi ba ne na yin watsi da wannan tsarin.
3. A rika godewa juna bisa kananan kyautatawa a tsakanin juna wanda ta haka ne Aboki/ Abokiyar zama za su rika mutunta juna. Kama daga ruwan wanka izuwa abinci daga abokin zama ya kasance akwai yabo a kan wannan aiki.
4. Kada ya kasance reno ko neman abinci ya dauke hankalin Aboki/ Abokiyar zama daga nunawa soyayya ta hanyar kusantar juna.
5. A rika ba juna lokaci na Wucin- gadi saboda a tsakanin abokan zama akwai bambancin ra'ayi da tunani wanda ta haka za su rika saukin juna.
6. Akwai bukatar kebe lokaci don wasa da juna ba tare da 'ya'ya a kusa ba wanda shi ma ta haka ne za su more rayuwarsu da kuma dangantakarsu.
7. A rika la'akari da dabi'un juna saboda kada a yi tunanin cewa wadannan dabi'u za su iya canja wa a tsawon lokacin zama. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C