Mata Na Samun Matsalar Kwakwalwa Idan Basa Saduwa Da maza Da yawa_inji Dakta Maimuna

A ranar Asabar ne wata likitar kwakwalwa mai suna Dr Maymunah Kadiri, ta shawarci matan aure da su yawaita jima'i da mazajensu don rage damuwa tare da samun farin ciki.

Kadiri, shugabar asibitin Pinnacle ta bada wannan shawarar ne a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai a garin Legas.
Kamar yadda ta ce, jima'i ba wai gyara jikin mace kawai yake ba, yana da matukar amfani ga lafiyar kwakwalwa.

"A matsayinmu na mata, akwai bukatar mazajenmu su zama aminanmu, matukar muna bukatar lafiyar kwakwalwa ingantacciya. Ilimi ne ya nuna cewa, matan da ke samun jima'i akai-akai basu cika samun damuwa ba idan aka danganta su da wadanda basu samu."

"Jima'i na da matukar amfani. Maganin matsanancin ciwon kai ne ga mata. Mace na fadawa damuwa matukar yawan jima'in da take samu ya ragu."

"Jima'i da yawa yana takar rawar gani wajen kara wa mace lafiyar kwakwalwa tare da ingantacciyar rayuwa."

Dr. Kadiri, ta kara da kira ga matan da ke da damuwa da su yawaita yin jima'i, lamarin na kara musu kima da lafiya. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C