Kungiyar Boko Haram Ta Yi Rashin Manyan Kwamandojinta

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa kungiyar Boko Haram ta yi rashin wasu manyan kwamandoji, makusanta ga shugaban kungiyar, Abubakar Shekau.
A cewar rundunar soji, an kashe manyan kwamandojin tare da sauran dumbin mayakan kungiyar Boko Haram yayin wata musayar wuta mai zafi da aka yi tsakaninsu a ranar 26 ga watan Mayu.
An yi musayar wutar ne bayan reshe ya juye da mujiya a harin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka kai a kan rundunar soji a kwanar Banki.
Daga cikin gagararrun kwamandojin kungiyar Boko Haram da dakarun soji su ka kashe akwai; Manzar Halid, Abu Fatima.
Wata majiyar rundunar soji mai tushe ta tabbatar da cewa an kashe mambobin kungiyar Boko Haram 70 tare da wasu manyan kwamandojin kungiyar irinsu ABu Jamratul Al-Naweer, Kaka Bana da Tareta Babakari.
Kazalika, sojoji sun kwace kayayyaki da makaman mayakan kungiyar da su ka hada da motocin yaki, babura da Kekuna.
Sojoji sun lalata kayayyakin da makaman a yayin da mayakan kungiyar Boko Haram su ka janye jiki tare da tarwatsewa zuwa cikin jeji.
Rundunar soji ta ce sahihan bayanai sun tabbatar ma ta da cewa kungiyar Boko Haram ta na cikin tsaka mai wuya, lamarin da ya hanasu sukunin tsara kai hare - hare saboda asarar mayaka da kayan aiki da su ka tafka.
Toshewa Boko Haram hanyoyin leken asiri, hanyoyin sadarwa da hanyoyin safara da rundunar soji ta yi ya gurgunta harkokin kungiyar Boko Haram tare da sanyaya gwuiwarsu wajen kai hari a kan jami'an tsaro. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C