Ku Kalli Bala'in Da Ke Tattare Da Zawarci

Zawarci Yana Da Daci A Zukatan Zawarawa.
NAYI NAZARI AKAN MATA DA MAZA
Wallahi Da Rayuwar Zawarci Gara Jinkirin
Aure Ga Budurwa.
A Gidajen Talakawa Kuncin Rayuwar Zawarci Shike Jefa Dayawa Daga Zawarawa Fadawa Cikin Karuwanci Don Nema Ma Kansu Abin Biyan Buqatar Rayuwa.
A Lokacin Da Mace Takasance Bazawara ACikin GidanSu Kannenta Zasu Rinqa Yimata Kallon Hadarin Kaji, Kuma Ta Samu Incin Yawo Guri-Guri Domin A Lokacin Ba Kowa Bane Zai Iya Tsawata Mata Ba.
Manzon Allah (s w s) Yace "Ku Tausayama
Wanda Yayi Arziki Amma Arzikin Yaqare"
Don Haka Yakamata Mu Tausayawa Zawarawa.
Shin!! Wai Mike Jefa Mata A Rayuwar Zawarci???
1 •Rashin Bincike Kafin Aure:
2 •Wani dan shaye-shayene
3 •Wani dan caca ne
4 •Wani baida hakuri
5 •Wani barawone.
6 •Rashin Haquri:
7 •Wata Rashin son zama da Kishiya
8 •Wata Yawan Gulma
9 •Raina miji.
10 •Wasu Kuma Mazanne Masu Auri Saki.
11 •Wasu Kuma Mutuwace Ke Yanke
Kaunar. ALLAH ka tsare muna imaninmu da mutuncinmu da addininmu ALLAH kasa mufi karfin zuciyoyinmu kabamu ikon hadiye kwadayinmu kada kwadayi ya hade mu.
MATA GA SHAWARA KYAUTA
" So Don sha'awa mafi yawan Mazan yanzu suke yi muku" maganar kenan dai to tambaya? Ta yaya Namiji zai dinga Sonki don Sha'awa ba tare daya san Surar jikinki ba ?
Ko kina aikata masa wasu Abubuwa wanda suke fitinar zuciyarsa,Shin shi Katako ne? Me yasa bakya kiyaye duk waɗannan a matsayin ki na MACE?
Ki gwada Nuna masa So don Allah mana,ki gwada nuna masa Allah,ki gwada nuna masa Hanyar Haramci da Halacci,ki gwada yi masa Nasiha idan kika ga yana so ya kufce,ki gwada Dagewa kan Ku haɗu kuji tsoron Allah,kiga ko bai chanja Hali ba,kiga ko bai Soki da zuciya ɗaya ba,ki gwada Dagewa kan Baza ki aikata wasu abubuwa ba don farincikinsa indai Allah baya so ki gani ko bazai koya ba,ki dinga Ɗaga qafa wasu lokutan ki mantar dashi dukkan wata Damuwarsa ki rarrasheshi da kalmomi masu sanyi da nuna masa So ne yasa duk kike masa wannan,bakya Son ku rasa duk wata Albarka.
Indai zaki dinga yin waɗannan Abubuwan Haqiqa indai yana Sonki da gaskiya har cikin zuciyarsa zai Kasance yanda kike so,musamman idan zaki dinga amfani da Hikima sosai.
To amma inaaa! Ke kanki Baki koyi Juriya da Tarbiyyantar da kanki ba da Nuna A'A da babban Harafi, tayaya shi zai dinga kiyayewa kina buɗe masa Qofofi?? Dole Dole kece Mace,ba saurayi ba ko Miji sai kin koya masa wasu Abubuwan kafin ya saba dasu kuma ya koyes,balle wanda da kin bayar da wata dama zaki gundiresa ya tafi ya barki da cizon Yatsa.
Wannan yasa Dole mazan yau su dinga yin SO don sha'awa,saboda matan ke Bayar da Qofa,suna rura wuta,koda da farko don Allah suke yi yau da Gobe sai a rasa wanda zai nunawa wani hanyar Allah ayi ta soyewa har a Qone
tunda hakan aka Bawa juna Tarbiyya.
Idan kika bi Hanyar Allah kika ga ya dage yafi son Hanyar shaiɗan sai ki rabu dashi,dama ba kalarki bane ,sai ya qara Gaba,kiyi fatan Allah ya kawo miki wanda ya fishi Alkhairi Duniya da Lahira.
Amma ya kauce kin Bisa,shi ina Ruwansa kefa macece.Allah ya gyara mana.Ameen. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C