Ko Kun San Lalacewar ‘Yan Mata Laifin Waye?

Kafin yanzu muna kallon mace mai bin maza ita ta fi kowace mace lalacewa a duniya. Amma a halin da ake ciki yanzu mun zo wani zamani wandaa wurin ‘yan mata shaye shaye da mad’igo shine wayewa.
Tun suna yin abinsu a boye har abin ya fito fili domin idan yarinya tana irin wannan harkar za ka ga kowa ya sani har misali ake yi da ita ana nunata a unguwa.
Munin wannan harkar ta sa ‘yan mata yanzu ba su da kunya kuma sun daina mu’amula da maza sai dai su dinga kula mata ‘yan uwansu.
A shekaru da dama da suka wuce ana danganta ‘yan mata masu harkar mad’igo sun dauko wannan dabi’ar daga boarding school ne.
To amma yanzu abin da zai baka mamaki ‘yan mata masu matsakaicin shekaru wadanda suke karatun boko da islamiya gaban iyayensu zaka ji labarin a cikin gari cewa tana daga cikin masu irin wannan dabi’ar.
Iyaye da shuwagabanni sun kasa mayar da
hankulansu domin a shawo kan wannan matsalar wacce ta zama ruwan dare gama duniya. An saido tarbiyyar ‘ya ya mata sai qara lalacewa take yi fiye da tunanin mai tunani wai har lalacewar ta kai ana kunnen doki tsakanin ‘yan mata da samari wurin mummunan dabi’u.
Idan har da gaske ana so a shawo kan wannan matsalar to fa dole sai an bi wadannan hanyoyin sannan :-
✧– Dole iyaye su sa ido akan su waye qawayen’ yar su… Matuqar basu gamsu da wadannan qawayen ba to su gimtse wannan alakar.
✧– Handset, musamman Android domin ita ce babbar hanya mafi saurin lalata tarbiya… Da waya za’a hurewa yarinya kunne kuma da ita za a kira ta ta je kuma da waya ce za a fara turo mata wasu hotuna ko bidiyo masu nuna tsiraici har sha’awarta ta motsa. Saboda haka ya kamata a daina barin ‘yan mata suna rike waya.
Idan kuma rike wayar ya zama dole to a bata karamawacce zata amsa kira kawai.
✧– Fita ba bisa qa’ida ba. Kullum iyaye suna kallo yarinya zata dauki hijabi ta fita akan wani dalili wanda bai zama dole sai ta fita din ba… Idan ta fita shikenan duk inda ta ga dama zata leka kuma sai lokacin da ta ga dama zata dawo.
✧– Yarinya ta shigo da babbar kyauta da sunan
kawa ko saurayi ya bata. Lallai a dakatar da yarinyar daga amsar irin babbar kyauta daga hannun ko waye.
Lallai yakamata iyaye su saka idanu kuma su kula da kiwon da Allah ya basu akan ‘ya’yansu domin wallahi rashin sa’ ido da rashin bibiyar halin da ‘ya’ yanmu ke ciki ya sa ‘yan matan ga halaka.
Jiya wani yana bani labari yace wallahi akwai hotel din da mata ke kamawa mata ‘yan uwansu d’aki. Daga baya da masu hotel din suka lura sai suka sa dokar hana mata d’aki. Yanzu cewa ya yi matan da suka fahimci haka sai su kira namiji su bashi kudi ya tafi ya kama musu d’aki su bashi ladanshi. Ya ce kuma ba wai ‘yan mata kawai ba ya ce har da matan aure da zawarawa.
Haka dai wani yana bani labarin ya ce jiya jiyan nan wata ke bashi labarin cewa kawarsu wata ta yi mata sayayya ta fi ta dubu d’ari ciki har da sutura kala 12.
To wallahi idan za mu farka mu
farka domin wannan al’amari qara gaba yake yi.
Zaka ga yarinya mai nutsuwa da tarbiya ba ta kula samari amma daga baya ta fada tarkon wadannan mutanen ta hanyar jan hankalinta da abin duniya.
Wasu ‘yan matan kuma sharri ake musu dan kawai a bata musu suna ko kuma dan suna qawance da wacce take yi ko ake zargi…
Lallai mata ku kula domin watarana ku iyaye ne kuma ku ne makarantar farko… Ya kenan tarbiyyar ‘ya’yanki zai kasance idan aka ce kina da irin wadannan munanen dabi’un? 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C