Ko Kun San Alamomin Mace Mai Kishin Kanta?

Wanka:
Mace mai kishin kanta za'a samu tanayin wanka akalla sau biyu a rana, kada kiyi zatan mijinki zaiji shaawar kusantarki idan kika kasance da safe idan kin tashi zaki Shiga bandaki ki amfani da toilet, kiyi fitsari, kidawo gado ki rabeshi da gumi da warin jiki. Kuma ki tunanin zai wasa da jikinki da ya farka a bacci.
Ki tashi da wuri kafin ya tashi ki wanka ki wanke jikinki ki fesa turare ki canja dressing dinki sannan ki dawo gado jikinshi kina kamshi, anan zakiga soyayya mai karfi, ba tareda kin shirya mata ba ko ya shirya mata.
Shaving:
Mace mai aji anaso ta yawaita aske gashin jikinta, musamman na Hammata Dana gabanta, wasu Matan idan sun haihu dayawa sukan daina aske gashin jikinsu musamman na gabansu, cewa ai su sun girma sun haifi yara dayawa, sai subar gashin gabansu ya zama Kamar yayi ba kula kuma a haka sukeso mazajensu su rabesu. Wannan ya fi karfi a cikin Matan hausawa, gashi yana jawo zafi wanda za'a sami gumi da zai haddasa miki warin gaba, danhaka ki kiyaye.
Iya da kaya
Ki iya Shiga mai kyau wadda zaki fito fes kina kamshi yanda duk namijin daya ganki zaiga kinyi kyau kin iya Shiga da sutura mai tsafta, wasu Matan Dan sunyi aure saisu yi Shiga Kamar wata mahaukaciya ko tsohuwar mace da ba aure gareta ba, kada kuma kiyi shigarda zaki fidda tsiraicin jikinki ko wadda addini ya hana, akwai Shiga da zaki Wanda jikinki kadai zaki iya yiwa wannan babu laifi. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C