Karki Tsaya Sai Namiji Yazo Neman Aurenki, Idan Kikaga Wanda Yamaki Nemeshi Kuyi Aure

Karki Tsaya Sai Namiji Yazo Neman Aurenki, Idan Kikaga Wanda Yamaki Nemeshi Kuyi Aure.

Wani Dan uwa musulmi mai suna Muhammad Habeebulahi Oladele, ya shawarci yan matan da basuda samaran dazasu aura da kada su tsaya jiran sai Namiji yazo akan suyi aure.

Ya bayyana haka ne a shafinsa na fesbuk a yayinda yake bada shawarar inda yace babu laifi ga mace musulma wacce takai shekarun aure, akan ta nemi wanda takeso ta aura ta shaida masa idan ta yaba da halayensa.

Yace ya halasta ga mace musulma ta shaidawa wanda takeso ta aura bukatar aurensa, ya kara da shawartar mata akan cewa idan wanda kike son aura baya da halin auren to zaki ki iya daukar dauyin auren idan kinada halin haka.

A matsayinki na budurwa marar aure,  karki tsaya jiran wai sai mijin aure yazo nemanki, ki tsufa, a a kije ki nemi kamilin mutum akan ku hada hannu Kuyi aure hakan ya halasta a muslunce.

Idan attajira kike kinada hali to kidauke dauyin dawainiyar auren,  idan kuma bakida halin daukar dauyin dawainiyar auren to ki saukaka masa yadda auren zaiyi sauki batareda azabtar da mijin ba.

Yin hakan yafi zaman ki gida ke kadai babu mijin aure, saboda idan ba Allah yakare kiba dadewa ba auren kan iya jefa ki zinace zinace , wanda hakan zai iya kaiki wuta, Allah ya tsare.

Hadisi ya inganta , ummuna Khadijah (Radiyallahu anha)  ta nemi  fiyayyen halitta annabi Muhammad (S. A. W) akan ya aureta, kuma ya amsa bukatar ta ya aureta.

Allah ya saukakawa mazajen mu da matayen mu maso son aure, ka aurar dasu, Ameen

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C