Ka bamu kunya' - Dattijan arewa sun caccaki shugaba Buhari

Kungiyar dattijan arewa (NEF) ta koka a kan halin rashin tsaro da arewa ke ciki tare da zargin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da gaza yin maganin matsalar.
A cikin wani jawabi da ya fito ranar Lahadi, jagoran kungiyar, Ango Abdullahi, ya ce lamari rashin tsaro ya na kara tabarbarewa a kullum.
Ya ce yawaitar hare - haren 'yan bindiga da mayakan kungiyar Boko Haram ke kaiwa alama ce da ke nuna cewa gwamnatin Buhari "ta fadi kasa warwas" a bangaren tsaro da walwalar 'yan kasa.
"Kungiyar dattijan arewa ta damu matuka a kan yawaitar hare - hare da asarar dukiya a yankin arewacin Najeriya.
"Yadda 'yan bindiga suke cin karensu babu babbaka ya nuna cewa yanzu yankin arewacin Najeriya yana hannun 'yan ta'adda, sai yadda suka ga dama suke yi.
"A bayyane take cewa gwamnatin Buhari da gwamnatocin jihohi sun rasa yadda zasu bullowa lamarin, sun gaza kare rantsuwar da suka yi a kan cewa zasu kare jama'a da dukiyoyinsu.
"Lamarin tsaro kullum kara tabarbarewa yake yi saboda 'yan ta'adda sun fahimci cewa akwai raunin shugabanci a wannan gwamnati, lamarin da ya basu karfin gwuiwar kai munanan hare - hare a kan jama'a," a cewarsa.
Farfesa Ango ya bayyana cewa arewacin Najeriya bai taba shiga cikin yanayin rashin tsaro kamar na wannan lokacin ba tare da zargin shugaba Buhari da daukan alkawuran da basa sauya komai.
"Lokaci ya yi, tura ta kai bango. An san mutanen arewa da hakuri da girmama doka da shugabanni, amma ya kamata gwamnatoci su sani cewa hakurin jama'a ya kare.
"Mu na sane da cewa wasu 'yan arewa na shirin gudanar da zanga - zangar lumana, kamar yadda kundin tsarin mulki ya basu dama da 'yanci, domin jawo hankalin shugaba Buhari da sauran shugabanni a kan halin da suke ciki a arewa," a cewar Farfesa Ango. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C