Hanyoyi Guda Shida (6) Na Magance Yaduwar Gulma

Gulma tana nufin yada maganganu da aiyukan mutane a tsakanin mutane da niyyar bata su da aibanta su a tsakanin mutane,idan aikin ko maganar da kafada haline nasa to wannan shine gulma,amma idan abinda kafada karyace,to wannan sunansa KAGE da Bata mutum yafi Gulma da Muni da girman Hakki awajan Allah.
Gulma tana cikin manya manyan zunubai da suke halaka al'umma kuma tana cikin laifukan da Allah baya yafewa Saboda akwai hakkin bawa acikinsa,kuma gulma tana cikin manya manyan zunubai da suke janyowa mai yinta ayi masa azaba a qabarinsa.
HANYAR MAGANIN MAI KAWO MAKA GULMAR MUTANE
Duk wanda ya kawo maka Gulmar wannan akwai abubuwa guda shida da suka zama wajibi akanka:

1-Kada ka Gaskatashi acikin labarin gulmar da ya kawo maka*. Kuma kada ka yarda da abinda zai fadamaka, domin mai yawo da gulmar mutane Fasikine shi acikin musulcin kowane,kuma ba karbar shedarsa saboda fadar Allaha acikin Suratul Hujraat: ( (  ﺃَﻳُّﻬَﺎ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﺁﻣَﻨُﻮﺍ ﺇِﻥْ ﺟَﺎﺀَﻛُﻢْ ﻓَﺎﺳِﻖٌ ﺑِﻨَﺒَﺈٍ ﻓَﺘَﺒَﻴَّﻨُﻮﺍ ﺃَﻥْ ﺗُﺼِﻴﺒُﻮﺍ ﻗَﻮْﻣًﺎ ﺑِﺠَﻬَﺎﻟَﺔٍ ﻓَﺘُﺼْﺒِﺤُﻮﺍ ﻋَﻠَﻰٰ ﻣَﺎ ﻓَﻌَﻠْﺘُﻢْ ﻧَﺎﺩِﻣِﻴﻦَ ) [Surat Al-Hujraat : 6]
awannan Aya Allah ya nuna mana karara cewa mai yawo da labarin mutane na gulma Fasikine. 

2-Ka haneshi akan wannan gulmar da yazo maka dashi ,kuma kayi masa nasiha,kuma ka bayyana masa munin abinda yake aikatawa. saboda da fadan Allah: ( ﻳَﺎ ﺑُﻨَﻲَّ ﺃَﻗِﻢِ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺃْﻣُﺮْ ﺑِﺎﻟْﻤَﻌْﺮُﻭﻑِ ﻭَﺍﻧْﻪَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻤُﻨْﻜَﺮِ ﻭَﺍﺻْﺒِﺮْ ﻋَﻠَﻰٰ ﻣَﺎ ﺃَﺻَﺎﺑَﻚَ ۖ ﺇِﻥَّ ﺫَٰﻟِﻚَ ﻣِﻦْ ﻋَﺰْﻡِ ﺍﻟْﺄُﻣُﻮﺭِ ) [Surat Luqman : 17]
awannan ayar Allah ya bayyana mana acikin Qissar Luqman cewa kayi umarni da kyakjyawan aiki kuma kayi hani da mummunan aiki. Annabi s.a.w yana cewa: 
Duk wanda yaga abinki daga cikinku to ya chanzasa da hannunsa, idan bai sami ikoba to da bakinsa.........
Muslim

3-Kayi Fishi da shi dan Allah saboda abinda ya aikata,ba dan wani abu da ban ba.

4-Kada kayi mummunan zato ga dan uwanka da aka kawo maka gulmarsa.saboda Fadar Allah Ta'ala: *( ﻟَﻮْﻟَﺎ ﺇِﺫْ ﺳَﻤِﻌْﺘُﻤُﻮﻩُ ﻇَﻦَّ ﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﻭَﺍﻟْﻤُﺆْﻣِﻨَﺎﺕُ ﺑِﺄَﻧْﻔُﺴِﻬِﻢْ ﺧَﻴْﺮًﺍ ﻭَﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﻫَٰﺬَﺍ ﺇِﻓْﻚٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ ) [Surat An-Noor : 12]*
Awannan Aya Allah yana tsawatar da mu akan yiwa yan uwanmu zato kyakkyawa. Kuma Annabi s.a.w yana cewa: Ku riqa yiwa yan uwanku zato na alkhairi.

5-Kada ya daukeka ka rudu akan yin bincike akan abinda aka fada dakuma neman tabbatar da ahakan ya faru ko kuma ba hakabane. 

6-Kada kayi kokarin yada abinda ya fada sai kaima kazama kamarsa. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C