Hanyoyi Biyar (5) Da Mace Zata Mallaki Miji Cikin Sauki

Kamar yadda kuka sani yana daga cikin halayyar mata, neman hanyar da su mallaki miji. Irin wannan lamari kan ba wasu mata matsala wajen gane yadda za su bi su mallaki miji cikin sauki.
Wasu daga ciki gani suke, zuwa wurin boka ko malam a samu wasu siddabaru a matsayin taimako domin mallake miji shi ya fi sauki.
Mata ga hanyoyi mafi sauki na mallakar miji wanda aka tsara bisa koyarwa manzo:
1. Ya kasance duk magana da zai fita daga bakinki mai dadi ne a kunnen mijinki wanda zai sa shi murmushi da jin dadi.
2. Ki kasance a kullum kin dauki mijinki tamkar sarki ne ta wurin mutunta shi, da juriya wajen daukar laifinsa ya dawo kanki saboda bashi girma ko da ke ce da gaskiya.
3. Ki kasance mai sakin fuska ga mijinki a duk lokacin da ya shigo gida ya same ki cikin frinciki ko da akasin haka ne.
4. Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai sabawa wa addini ba ki yi mishi.
5. Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi shi ne kofa na kowane sharri. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C