Hadarin Dake Tattare Da Mace Ko Namiji Masu Auren DanDano

Namiji mai auren ɗandano shine namijin da zai iya kashe ko nawane na dukiya idan yanada su domin ya auri mace yayi jima'i da ita sau ɗaya kawai daga wannan kuma shekenan ta fice masa a rai.

Ana samun maza mazinatan da suna iya bata lokaci mai tsawo akan mace, kuma su kashe mata kudi masu yawa burinsu shine kawai ta bada haɗin kai sau daya tal daga nan ko ganinta bai so ya sake yi.

Irin waɗannan masu wannan ɗabi'ar akwai cikin mata. Masu wannan hali babu soyayya irin wanda Allah Ya saka tsakanin mace da miji. Sai dai Zukatan su cike take da sha'awa na jima'i.

Malaman jima'i sun tabbatar da cewa a duk cikin mutane goma na taron maza ko mata, ana iya samu mutum guda dake da irin wannan halin.

Illar da irin waɗannan mutane suke dashi bai ma tsaya a aure kadai ba, hatta a zina suna iya cutar da waɗanda suka kamu da sonsu, ganin daga wannan lokacin da suka gama ba zata sake yarda su sake yi ba koda kuwa zasu hadu so goma.

Haka idan namiji ne mai halin. Wanda haka yakan sa wanda ya kamun da soyayyar irinsu zai iya shiga kunci da damuwa na wani lokaci.

Irin waɗannan mutane sunada wata baiwa na daban da duk lokacin da suka sadu da mutu to fa dole ne sai yaji yana matukar sonta ko taji tana matukar sonsa. Amma duk a banza saboda daga wannan lokacin yana da wahala a sake yi koda kuwa za a sake haduwa.

A bangaren aure kuma idan macece dake da wannan halin to fa mijin duk lokacin da yake bukatar saduwa da ita sai ya sha wahala wajen shawo kanta. Kuma idan har ba hakura yayi da kauda kai daga wasu abubuwa ba zai iya sakin ta cikin ƙaramin lokaci. Don haka nema bincike ya tabbatar da kashi 30 cikin 100 na matan aure mazinata irin waɗannan matan ne.

Illar maza mãsu irin wannan hali daga daren farkon da suka gama saduwa da amaryarsu, daga wannan lokacin zaki soma ganin sauyi. Idan har bai yi saurin sakin ta ba to zai rika daukar lokaci mai tsawo kamin ya sadu da ita.

Kuma a kullum hankalin sa yana kan wasu matan a waje.
Babban matsalar da mace ko namiji zasu iya fuskanta shine na rashin iya fahimtar irin waɗannan mutanen kamin aurensu. A darasi na gaba zamu kawo alamomin masu auren dandano.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C