Gwamnatin Tarayya Ta Sanarda Da Ranar Komawa Makarantu

Ma'aikatar ilimi ta tarayyya ta bayyana ranar 13 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a koma makarantu a fadin Nijeriya.
Sai dai komawar makarantun zai kasance ne ga 'yan ajin karshe na babbabar sakandire da wadanda za su rubuta jarabawar NECO da WAEC.
Sai Kuma 'yan aji 6 na firamare wadanda za su rubuta jarabawar shiga sakandire. 

Mun Kashe ‘Yan Ta'adda Guda 392 A Katsina, Mun Datse Hanyar Samun Kayan Amfanin Mayakan Boko Haram, Cewar Hedikwatar Tsaro Ta Kasa
Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa, a ci gaba da kai hare-hare da take yi ta sama da kasa akan Boko Haram hakika tana ci gaba da samun gagarumin nasara.
Hukumar ta bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin da ta samu sun hada da datse hanyar samun kayan amfanin Boko Haram, kashe wasu kwamandojin kungiyar da lalata wasu maboyarta.
Tace wannan nasara tasa kungiyar cikin rudani da riki wanda ta koma kai harin samame wanda kuma ana hana su samun nasara, karkashin Rundunar Operation Lafiya Dole.
A bangaren hari kan ‘yan ta’addar Katsina da Zamfara kuwa, hukumar sojin ta bayyana samun nasarar kashe 392 daga cikinsu wanda ta ce aikin yana gudana ne bisa hadin gwiwar wasu sauran jami’an tsaro.
Ta bayyana cewa tana tsaye kyam dan ganin ta samu nasara a wannan yaki, inda ta ce tana godiya ga sauran takwarorin tsaro da suke aiki tare kuma tana neman ci gaba da bada hadin kai daga jama’ar gari dan samun nasarar kawo karshen ‘yan bindigar. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C