Gwamnati Zata Samar Da Matasan manoma 100 a Dukkanin Kananan Hukumomi 774 Dake Najeriya

Gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta ta samar da matasan manoma 77,400 da zasu fito daga kananan hukumomi 774 dake fadin Najeriya.
Gwamnatin zata yi hakane a karkashin hukumar NALDA dake kula da filayen nema a Najeriya.

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangidane ya samar da wannan ma’aikata a shekarar 1992 amma a shekarar 2000, sai tsohon shugaban kasa,Olusegun Obasanjo ya kasheta.

Hawan shugaba kasa,Muhammadu Buhari sai ya dawo da wannan hukuma. Shugaban wannan hukuma, Paul Ikonne ya bayyana cewa zasu hada kai da gwamnoni dan samar da filayen da za’a yi amfani dasu wajan yin noman.

Yace suna so su saka matasa cikin harkar noma kodai kiwon dabbobi ko kuma noman hatsi. Yace zasu karfafa yin noman koda na neman kudi ne ko kuma dan amfanin kai.

Yace shirin wanda shine na farko da taimakon shugaba Buhari zai wakanane a tsawon watanni shida. Muna so mu samar da arziki ta hanyar boma ta yadda za’a rika fitar da albarkatun noma zuwa kasashen waje. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C