Duniya Ba Za Ta Koma Yadda Take Ba

Na san muna ta jira a gama Covid19 kamar yadda aka gama Ebola ko Lassa FEVER mu koma sha'anin mu kamar yadda muka saba ko?
Kwarai za a kammala Covid-19 ba da dadewa ba,kwayar cutar za ta mace a hannun magungunan da ake ta samarwa. Sai dai tasirinta na iya wanzuwa nan da shekaru dari masu zuwa in ba wani iko na MAI duka ba.
Me ya sa ba za a koma yadda ake ba kamar yadda aka yi zamanin Ebola? Tambayar kenan ko? Amsar ita ce Ebola kasashen Rabbana aatina ta kassara wadanda ko a Africa ma basu da farcen Susa, yayinda Covid19 kuwa kasashe ashirin masu makullan Sarrafa duniya ta makure wa wuya. Daga Babbar giwa China ta soma rarrafe sannan ta balaga a babbar Giwa Amurka bayan da ta saki rassa a kasashen G8 da Rasha
Amma Wane irin tasiri za ta iya bari bayan ta mutu wanda ko dan Adam ne ya mutu bai taba iya bari ba ballantana wata kwayar cutar da bata kai kwayar Zarra ba? Wannan ma tambaya ce, bari na lissafa amsoshin kamar haka
1 Zai yiwu an kawo karshen zama a Ofis a manyan kasashen duniya...Kamfanin Facebook da Goggle tuni suka bai wa ma'aikatansu hutun zuwa ofis har zuwa shekara ta 2021, wannan alama ce ta cewa kamfanoni da manyan ma'aikatu akan hanyarsu ta zuwa hutu sun fahimci cewa za a iya aiki daga gida, kenan babu bukatar tara manyan gine gine da biyan kudin wuta, kayan kyale kyale da kwamfutoci da dumbin haraji da ofis ke kallafa musu tunda ma'aikata za su iya aiki daga gida. Su ma ma'aikatan za su sami karin kudin kashewa idan aka cire musu kudin mota na zuwa ofis daga nauyin da suke dauka.
2 Manyan Birane za su dena samin cinkoso...kai zama su dena yi wa kauyuka tinkaho. Eh mana! Dama ofisoshin da suke da su ne ke janyo mutane su narka kudi don kama wani karamin daki da zaman mota don kawai a je ofis. Kenan mutum da ya baro kauye ya zo birni saboda aiki zai iya komawa kauyensa ba tare da ya rasa aikinsa ba tunda zai yi a katon gidan da kudin dakin birni zai iya samar masa. Wannan zai sanya kauyuka su fara samin ababen more rayuwa muddin yayansu da suka dandana birmi za su dawo su nemi hakkinsu na rayuwa da walwala. Kenan za rasa cinkoso a irin Biranen New Delhi, New York, Beijin, da Moscow kamar yadda za a iya rasawa a Abuja da Lagos ko Qahira da Iskandariya, ko Cape town da Johannesburg a nan Africa
3 Makarantu na iya komawa yanar gizo. Tun da aka fara Covid19 makarantu da dama sun karye bayan da aka rufe su iyaye ba za su biya kudin 3rd term ba. Sannan a Dole sun kirkiri dakunan karatu na yanar gizo don iya tsira da dalibansu ko ba ko sisi. Garin haka iyayen sun fahimci za su iya sanya yayansu a makarantu masu tsadar gaske a zahiri tunda Yanar gizo zata rage farashin kudin makaranta, sannan su ma makarantun sun fahimci za su iya rage nauyin malamai da dakunan karatu tunda idan aji na daukar yara 20 da malamai biyu to a yanar gizo aji na iya daukar dalibai dubu20 da malami daya!
4 Hijira zata tsaya cak! Eh mana, muddin ina da kwakwalwa da zan iya aiki daga dakina me zai sanya sai na yi hijira daga Moriki zuwa Abuja, ko da ga Malawi zuwa Amurka? Saboda Dala? To ai za a biya ni da Dala a ko ina
5 Kudin takarda zai karasa mutuwa. Kwarai a zaman sama da sati biyar da kasashen duniya suka yi a kulle an sami karuwar kasuwancin yanar gizo inda maimakon samar da cinkoso a manyan shaguna sai aka rika aikin Delivery inda zaka bukaci abu shagon ya aiko maka. Ko a kasar nan da ba mu da jan wuya an yi cinikin kayan salla ta social media. Sannan kananan shaguna ma ko a nan Africa sun fi gane su rataye lambar Acc a gaban shago ka yi musu Transfer in ka sayi abu, saboda tsoron yada cutar ta hanyar kudin takarda. Hakan ya kara sanyawa burbushin Takarda da ake ta rajin batarwa nan da 2030 na iya tafiya kafin 2021
6 Fiye da kashi70 na gidajen karuwai na duniya na iya zama kufai. Kwarai ina nufin karuwanci zai yi mugun raguwa muddin mazaje suka dena hijirar neman aiki nesa da iyalansu wanda hakan ke sanya su zama kayan karau a hannun karuwai, sannan matan za su kara kaimi wajen sake mallakar zukatan mazansu da suka rasa a baya wanda hakan ya kashe musu gwiwa ta hanyar sallamawa. Su ma karuwan zasu nemi wasu sana'o'in muddin kudin shiga ya ragu
Me ake bukata ne don tarbar wannan sauyi hannu bibbiyu? Na san wasu za su ce 5G ake bukata kamar yadda labarai ke cewa dama shi ake son kaddamarwa ko? Ni dai ban sani ba, amma na san tabbas babu abinda ake bukata na karban wannan sauyi hannu bibbiyu sai Bisimillah da Karban kwakkwaran WIFI

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C