Coronavirus Ce Silar Rabin Mace-Macen Kano

Binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a Jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan biyo bayan mace-mace da ba a saba gani ba a jihar.

Ministan Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan ranar Litinin a wurin taron manema labarai na kullum da kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da korona ke yi a Abuja.

Ministan ya shaida wa manema labarai cewa kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen sun mutu ne sakamakon cutar korona, yayin da suke fama da wasu cutukan na daban.

A cewar ministan, an samu rahotonnin mutuwar ne a ƙaramar hukuma takwas na cikin birni a watan Afrilu.

Ya bayyana cewa an riƙa samun mutuwar mutum 43 a kullum lokacin da cutar na kan ƙololuwarta kafin daga bisani adadin ya zama mutum 11 a kowacce rana.

Ya ƙara da cewa kusan kashi 56 cikin 100 na mace-macen sun faru ne a gida, yayin da kashi 38 suka faru a asibiti.

Osagie ya ce mafi yawan waɗanda suka rasu shekarunsu sun zarta 65, inda ya ƙara da cewa akasarinsu sun rasu ne saboda rashin samun kulawar likita da aka saba ba su.

A baya dai gwamnatin jihar ta sha musanta cewa cutar korona ce take kashe mutanen.

Masana harkar lafiya a Kano sun bayyana fargaba bisa raguwar alƙaluman masu korona da ake fitarwa na baya-bayan nan daga jihar - wadda ta fi fama da annobar a arewacin Najeriya.

Ga alama tun daga Alhamis 21 ga watan Mayu lokacin da aka samu adadin mutum 28, ba a kuma fitar da alƙaluman masu cutar da suka kai yawan mutum 20 daga Kano ba har yanzu.

A ranar Alhamis ne Gwamna Ganduje ya ce za a fara bi gida-gida domin yi wa al'ummar jihar gwajin cutar korona.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C