Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

"So nake na samu budurwa danya sharaf na aura. Me zan yi da wannan bayan duk an gama da ita".Wadannan kalaman da ire irensu, shi ne zaki ji yana fitowa a bakunan mazan da suka tashi neman aure.
Ita dai budurwa itace macen dabata taba sanin da namiji ba ta harkar jima'i, ana nufin macen da azzakari bai taba shiga farjinta ba wannan ita ce ake kira budurwa a hausance. Sai dai kamar yadda na fada a rubuna na baya, mata da dama sukan rasa budurcinsu ne saboda wasu dalilai, wasu saboda yawan shekaru bayan sun kosa sun rika basu yi aure ba. Wasu matan motsa jiki ko yawan aikin gida ko tafiyar kasa yakan kawar masu da budurcinsu. Sai dai duk wata matan data rasa budurcinta ta wadannan hanyoyin ba daidai take ta macen data rasa budurcinta ta hanyar jima'i ba.
Idan kika kasa maza kashi dari, kashi 75 cikinsu babu abunda suke da buri illa a lokacin da suka tashi yin aure su auri budurwar da babu wanda ya taba saninta a jima'ince. Hakan a wajen maza wani abun alfahari ne da kambama kai ga magidanci ko saurayin da yayi sa'ar samun mace a hakan ya aura. Sai dai kuma mazan da suke da irin wadannan burin akasarinsu maza ne da idan da za'a bincikesu sai an samu wasu daga cikinsu sun taba zina da kananan 'yan mata, wasu ma sune suka soma yin zina da irin wadannan 'yan matan a rayuwarsu.
Yanzu haka al'uma gaba dayanta a wannan zamanin ta yi amanna da cewa, akasarin 'yan matan da suke gaban iyayensu, 'yan matane idan aka kasasu 100, to 80 daga cikinsu sun taba sanin da namiji, sunsan jima'i sunsan abunda iyayensu suka sani koma fiye. Wannan bazai zama gaskiya ba, kuma yana iya zama gaskiya saboda yadda zina a wannan lokacin ya zama abun ado, haka kuma 'yan matan sai sun kai munzalin wuce aure suke samun mazan aure, ga kuma yadda finafinai, littatafai da hotuna batsa masu motsa sha'awa suka ya waita a hannun 'yan mata. Amma duk da haka 'yan matan da basu taba sanin maza ba ta harkar zina suna nan da dama a gaban iyayensu.
Babu shakka mazan da suke lalata wadannan 'yan matan har kuma suka gujesu da sunan bazasu aure su ba saboda sun tashi daga budurci suke da laifi, amma kuma meyasa kamar yadda macen data rasa budurcinta ta hanyar jina batada mutunci a wajen maza masu neman aure, meyasa muma matan bazamu kyamaci duk namijin da muka san cewa mazinacine ba yasan 'yan mace bata fiskar aure ba? Mata da damar gaske da nayi musu irin wadannan tabbayar amsarsu bata wuce cewa, shi dana miji iskancinsa adone ba, ni kuma wannan hujjar da suke yawaita bani sai nake ganin cewa mu kammu mata mune muka kara ingiza kyayar 'ya'yan mu mata da maza suka zama abunda suka zama a yanzu. Domin babu inda Allah SWA ya nuna mana cewa a cikin Alkur'aninsa mai girma na miji yana da wani lasisin da zai iya aikata sabo ba tare da an kamasa akan wannan laifin ba, amma 'ya mace idan ta aikata tanada zunubi. Haka cikin hadisai ma babu, don haka mune ke tunzura maza suke yin abunda sukaga dama da 'ya'yan mu kuma daga karshe su watsar mana da su bayan sun gama lalata manasu su barmu da abunmu.
Babu wata tantama ko inkari, mazan da suke lalata 'yan mata yana da wuyar gaske kiga sun auresu, ko kuma sun bari wanin da suka sani ya aureta, haka nan ma da zai samu labarin cewa zata auri wani ko bai san wannan ba zai yi kokarin nuna masa cewa wannan ba macen aure bace ko da kuwa da karfin tsiya ne ya kwanta da ita ba da yardarta ba.
A kullum zina da kananan 'yan mata budurwai sai kara karuwa yake a cikin wannan al'uma, ganin yadda hakan ya zama wata masifa ga masu neman kananan 'yan mata da sunan tsafi ko kuma bala'in daurawa rai. "Yar uwa ko kin taba shiga manyan makarantu kasan nan kinga yadda maza masu kamada su shiga gaba suja sallah suke shiga domin neman kananan 'yan mata?
Bama ta wannan ba, 'yan matan gaba da sakandare dama 'yan mata ne da ake musu ganin cewa sun san komai, ki dawo makarantun furamari da kuma sakandare, inda muke yawan samun matsalolin na yadda ake yaudaran kananan 'yan mata tsofin suyi fasikanci da su. Wannan kuma yana faruwa ta yadda su kansu maza suka uzurawa ransu cewa sai sunyi zina da kananan yara, wasu lokutan 'yan matan da ake irin wannan lalatar da su basuma iya wankar tsarki barema su san ciwon kansu. Kuma bayn an lalata irin wadannan yara daga bisani kuma sai a tallatasu a duniya cewa ai ba matan aure bane.
A makon data gabata na samu wata matsala inda wata mace 'yar shekaru 27 da haihuwa ta zo har gidana domin neman shawara akan matsalar data shiga, wannan matsalar kuwa ita ce na wani saurayinta da suka yi kusan shekaru 7 suna soyayya, a wannan lokacin ne kuma ya koyamata zina kuma suka ci gaba da yi da sunan zai aureta, sai a makon data gabata ne ya fito mata muraran ya ce mata shi iyayensa sun hanashi auren macen data taba yin zina. Wannan maganar ya bakanta mata rai, don hakane tayi kokarin nuna masa cewa ita a duniya bata taba sanin wani da namiji ba banda shi, kuma wannan bazai hana ya aure taba amma yiki amincewa da bayaninta, don haka ne tazo domin na bata shawara kuma na bata.
Na taba samun makamancin irin wannan matsalar, inda ita wannan karamar yarinya 'yar shekaru 19, wani hamshakin mai kudi dan shekaru 50 da haihuwa ya nemeta da aure, ana cikin soyayya ne ya yaudareta yayi zina da ita, harma yayi mata ciki daga bisani aka zubar. Bayan da lokacin daya dauka na auren ya kusa ne yace mata shifa bazai iya aurenta ba ganin yanzu idanuwanta ya bude don haka shi budurwa yake so wacce batasan komai ba. Kuma abun mamaki wannan bawan Allah mutum ne da yake da 'ya'ya mata kuma ana ganinsa da matukar daraja a garin.
Yanzu haka nan da masu karatu suke karanta wannan mukalar, da akwai wata budurwa data ke dauke da cikin wani babba mai rike da mukami na siyasaa, inda wannan yallabai ya zoma mata da sigar aure, amma daga bisani ya jawo hankalinta da masu gidan rana har ya banka mata ciki, bayan cikin ya fitone kuma tayi masa magana yace shi bazai iya aurenta ba, sai dai zai bata kudi ko nawa ne taje ta zubar da cikin, laifinta anan ta bada kai bori ya hau, don haka shi yana neman budurwa ne wacce batasan komai bane ya aura. Sai dai kuma na bata shawarar abunda ya kamata tayi, duk da yake nasan wanda yayi wannan aika-aika ban nemi na bashi wata shawara ba, amma matakin da wacce yayiwa cikin take son dauka matakin ne da zai iya zubda mutuncinsa dama na gwamnatin dayake wakilta baki daya.
Ni ina ganin cewa, babu adalci kayi lalat da 'yar karamar yarinya har ka koyamata wani abunda bata sani ba a rayuwarta da sunan zaka aureta, daga bisani kuma ka watsar da ita da sunan cewa kai budurwa kake so. Ya kuma kamata 'yan mata su fahimci cewa, maza fa duk yadda kike sonsa da zaran kin bashi jikin da sunan zaki aureshi kin tashi daga aiki. Ya kamata al'uma ta fito karara ta kyamaci duk wani na miji mazinaci mai aure ko mara aure kamar yadda ake kyarmar auren budurwar macen data rasa budurcinta ta hanyar zina.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C