'Ba Zan Taɓa Mantawa Fa Waƙar Da Na Yi Wa Jonathan Ba'

Shahararren mawakin Hausa Nazifi Asnanic ya shaida wa manema labarai cewa a tarihin wakokinsa ba zai taba mantawa da wakar da ya yi wa tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ba.
Kodayake mawakin ya ce ya fi kaunar wakar da ya yi tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta 'Dawo-Dawo', amma wadda ya yi wa Jonathan ta tsaya matsa a rai saboda yanayin da ya shiga.
Mawakin ya bayyana hakan ne lokacin wata hira da muka yi da shi kai-tsaye a shafinmu na Instagram.
Ya ce bayan ya riga ya yi wa Jonathan waka ta yi karfi, sai ga shi kuma a shekarar 2015 yana so ya kara tsayawa takara "lokacin kuma masu son Buhari sun taru sun yi yawa."
Asnanic ya ce a lokacin ya shiga rudani saboda wakar Jonathan ta ƙi bacewa, "ga shi kuma muna son mu yi tallan Buhari. Wannan ya sa ba zan iya mantawa da wakar ba," in ji shi.
"Amma ni ban yi da-na-sanin yin wakar ba saboda ai a lokacin da na yi Jonathan ne ke mulki. Ina son wakar kuma ina son yadda na rubuta wakar."
Hakazalika shahararren mawakin ya ce wakar da yi wa Kwankwaso ba za ta taba bace masa a rai ba.
Ya ce yana jin dadin ta kuma yana alfahari da wannan ita. "Duk kasar da na je kafin a fada min wata waka, ita ake fara fada min." 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C