Alamomin Da Mutum Zai Ji Ya Fara Tunanin Yana Da Matsalar Raunin Mazakuta ?
1. Rashin Mikewar Azzakari; Haka na faruwa ko da an yi tunanin jima'i ko kuma ma an samu haduwar jikin mace da shi mai matsalar.
2. Saurin Kwantawar Azzakari; Abin nufi anan azzakarin zai mike sai dai ba da jimawa ba, sai ya kwanta, tun kafin aje ga saduwa ko kuma da zarar an fara.
A lura wannan na da banbanci da saurin kawowa, saboda anan za ta kwanta ne ba tare da mai matsalar ya kawo ba.
3. Rashin Sha'awa; Mai wannan matsala zai ji ba ya sha'awar saduwa da iyali. Ma'ana gaba daya sha'awarsa ta gushe.
Comments
Post a Comment