Al'adar Malam Bahaushe a gidan Aure

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Tsira da amincin su kara tabbata ga fiyayyen Halitta Annabi muhammad (s) da iyalan gidansa tsarkaka, wanda Allah ya aiko su da shiriya.
Mu'amalar aure a gidan Malam Bahaushe daban take. Babu jarabawa ga mata a wannan zamanin irin zamantakewar aure, musamnan a gidan Malam Bahaushe.
Shi kawai abin da ya dauki mace, shi ne wata aba ce da idan mutum ya na bukata zaije ga ita da zarar ya kammala biyan bukatarshi shikenan. Wani kuma ya dauki aure kamar saka Riga ne, duk sadda yaga dama zai cire, ma'ana ya sake ta.
Mace bata da wani 'yanci a gidan malam Bahaushe, illa iyaka tayi reno sai tuka tuwo, da sauran aiyukan gida. Bata da wani iko sai abin da maigida yace, ba a shawara da ita, bare ta bada a karba. Wani ma ganin yake ya zauna su Dan tattauna zata raina shi. Kawai sai abin da ya zartar a gidan.
Ita dai 'yar kallo ce! Duk wani hakki nata da 'yancin da Allah ya bata sai kaga duk an take mata. Sanan nen abu ne ga kowannemu cewa Allah ya yi hani ga zalunci. Kuma yana son masu tausayi da yafiya.
Addinin Musulunci yafi ko wanne addini bawa macce gata da kariya, Amma musulman sun fi kowa sakin auren da musgunawa Mata a gidan aure "especially" Malam Bahaushe Kuma a hakan muke so muyi ta zama mu na rayuwa?
Na taba tambayar wani cewa mai yasa musgunawa da rashin 'yanci da yawan sakin aure yafi yawa ga Malam Bahaushe? ganin yadda addinin musulci yazo mana da yadda za'a zauna a kyautatawa juna, So da kyauna da rikon amana, da sauke hakkokin juna da dai sauransu. Sai yace min “al'adarce haka”.
Subhanallah!
Kai malam Bahaushe ka saba wa umarnin Allah Amma kai kana son abi umarninka sannan ayi maka biyayya.
Na'am! Manzon Allah ya yi umarni mace tabi mijinta sauda kafa Matukar ba sabon Allah yake umartanta dashi ba.
Ya kamata Malam Bahaushe ya sani matar da ka aurar ba baiwa bace. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C