Al'adar Malam Bahaushe A Gidan Aure Kashi Na Biyu (2)

Duk da wasu mazajen sun yi ta yi mini martani akan rubutun da na yi waccan, amma wannan ba zai zama na bar abin da na ɗauka zan yi ba.
Duk lokacin da ake magana akan gyara, kamata ya yi a cire son rai, kowannen mu ya duba yaga ta ina ya kaza, sai ya yi ƙoƙarin gyarawa, ko da kuwa ana magana da wani ɓangare ne.
Tunda ai ana magana ne akan matsala ya ya kuma za a gyara. Amma idan kowa zai rinƙa duba cewa ai suma dayan bangare suna da kuskure laifinsu ne, toh! da sauran rina a kaba. Idan kowannenmu ya gamsu, ya duba inda yake da kuskuren ya ji zai gyara tabbas za a samu canji.
Zaman ibada ce! Indai dagaske ibadar mukeyi, kuma Allah muka nufa, sai mun cire son rai ga girman kai da Alfahari.
Ba nace mata ba su da matsala bane a zaman aure ba, sai dai kaso mai yawa na matsalolin suna gangarowa daga mazan ne ( ku gafarceni burazu)
Saboda Allah maɗaukakin sarki ya girmama maza a matsayin sune shugabanni a gidajensu. Su kuma mata sai Allah ya yi su da rauni. To ya kake tsammani idan ka ga da ƙarfi da kuma ikon shugabanci, sannan a baka amanar mai rauna ki?
Saboda haka mace a gidan Bahaushe bai kamata ta zama dabam ba, tana da haƙƙi ba kamar yadda a al'ada aka mai da ta sai kace baiwa ko yar aiki ba.
Idan muna fatan samun gida nagari dole mazan Hausawa su ɗauki matan su a matsayin ƙawayensu ne kuma abokan rayuwarsu. Wannan kuwa za a iya cimma nasara ta hanyar nuna ƙauna ga mace ba irin soyayyar I love you akan titi ba, amma idan an je gida sai muzurai da tsawa musamman lokacin da kowa ya gama sanin kowa.
Sannan damuwa da damuwarta na daga cikin abubuwan da za suke kawo shakuwa da juna. Wanda mutum ba zai gane damuwar matarsa ba matukar bai nazarci abin da zuciyar ta take so ba ko kuma take ki ba.
Sannan uwa uba, nuna soyayya wanda babu shakka an bar Malam Bahaushe a baya. Domin gidan da babu soyayya a cikinsa ga mace ba shi da mararraba da kurkuku. Ko da kuwa da kayan alatu a gidan.
Babu abin da yafi jin daɗi da burgewa ga mace fiye da mijinta ya dinga nuna mata kauna. Ita kuwa nuna wannan ƙauna ta ɗauki ɓangarori dabam dabam. Misali, furta kalmomin soyayya gareta, wannan kuwa ya haɗa da ko da yi mata gaisuwa ne. Wanda wasu Hausawan sun jahilci hakan a zamantakewarsu.
Mutunta abubuwa masu ƙyau da take so, da kuma gwada mata Kyakkyawar mu'amala. Wani ƙalubalen da ya kamata mu guje shi wanda akasari zamantakewar Hausawa ya yi kaurin suna da shi kuma sanadiyyarsa, aure da dama sun mutu sune yawan korafi, akan wasu abubuwan da basu kai sun kawo ba da kuma bibiyar laifuka.
Kuskuren da ya kamata a kawar masa da kai sai kaga maigida yana ta da jijiyar wuya akansa.
Fatan mu shi ne kawo gyara a duniyar zamantakewar bahaushe domin duniya ta ci gaba a fannin aure ta bar wannan ƙabila ta mu a baya. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C