Abubuwan Da Mata Ke Anfani Dasu Wajan Janyo Hankalin Mazaje

Akwai wani lokacin da zaka ga mace Tana son namiji bai kula da hakan ba, Ko da kuwa ta cika kowacce ka'ida ta zamantowa mace, Don haka zata iya bin wasu matakai Na Jan hankalin Sa.

Amma Kuma akwai abubuwan da Kai tsaye da maza Har su kan so suga mace Tana dashi.

Ilimi・biyayya・kunya・wayewa・hikima・fasaha・iya girki・tattali・tsabta・natsuwa・kissa・gwaninta kan shimfida ・dattijantakar iyayensu・

Wadannan su kan janyo hankalin namiji dawo yana sonta Har a ga kamar ta mallakeshi.

ILIMI

zaku ji muna ta magana a kan ilimi,to tamkar kwano ne babu murfi, zata yi ta abubuwa irin Na jahilai a zamantakewar aurenta, Wanda zai sanya duk son da namiji yake Mata za'a wayi gari yaji ya tsaneta, baya kaunar ganinta, idan Kuma Tana da ilimi Ko da miji baya sonta yanayin gudanar da rayuwarta zai sanya ta fara birge shi Har a wayi gari yana  sonta.

Don haka ya kamata Mata su tsaya gurin Neman ilimi Na addini Dana zamanin.

BIYAYYA

Mace Mai biyayya itace ke mallake miji ta sarrafashi yanda takeso cikin ruwan sanyi, domin duk Abinda ya sanya ta bata ketarewa hakan zai sanya shima ya dinga taka tsan-tsan da lamuranta.

KUNYA

Ana son mace ta zamo Mai Kunya, Kada ta dinga yin komai gatsar babu Kunya Ko maganganu batsa, ya kamata Ko kallon mijinta zata yi ta dinga jin kunyarsa Kada ta dinga ware masa ido irin kallo "yan Tasha Ko da kuwa sun shekara nawa ne.

Kada Kuma ta dinga sakin jikinta Ko da yaushe a gabansa, wani lokacin ta dinga nuna Tana jin kunyarsa, musamman gurin kallo ta Dan dauke kanta hakan ya kan sanya ta motsa namiji sosai.

WAYEWA

zaka samu wata macen tana da ilimi Amma babu wayewa.

Sai dai ita wayewa wani jigo Ce dake sanya mace ta sami miji a Hannu yanda ya dace, domin Tana da wayewar da duk zamanin yazo da ita za'a tafi.

Zaka samu mace wai Tana maganar ta waye Amma zaka ganta da ( kazanta idan ta haihu- maganganu mara dadi ga miji- wulakanta miji)

Haka Dinki da yanayin shiga rashin wayewa ke Maida mace gidahuma.

HIKIMA 

Ku San ita za'a iya cewa da ita ake halittar Dan Adam, Amma duk da hakan akan yi kokarin koyonta.

Mace Mai hikima da dabara bata da wahalar mallake namiji, Kai hanta abokan zama da dangin miji Tana hikimar zama dasu Don haka ya dace kowacce mace ta kasance Mai hikima da dabara zama da miji.

FASAHA

Banbancin su da hikima kalilan ne, ita fasaha itace ta kirkirar Abu

Ana son mace Kullum ta kasance Mai fasahar kirkirar abubuwa da zai farar ta rai mijinki

IYA GIRKI

Ku San wannan shine kashi ashirin da biyar Ko hamshin Na zaman aure, domin shike sanya miji kaunar cin abincin mace harma ya dinga alfahari da ita.

ABUBUWA DA MATA SUKA FI BUKATA A GURIN NAMIJI DA ZASU AURA.

Wadata・asali・jarumta・kyau・shahara/daukaka・tsaka-tsaki・ilimi・kudi.

Wadata

Mata suna son namiji Mai wadata, Wanda yake da halin iya dauke dukkan wata bukata.

Sai dai Ana son idan mace zata tayi aure Kada ta sanya son kudi da Neman abin duniya kawai a ranta, ya kamata tayi addu'a Neman zabin Allah, domin wani lokacin auren wadata idan ba ilimi bane ya kan zo da matsala.

ASALI

Mata suna son namiji Dan asali Wanda ya fito daga gidan asali, Mai nagarta, domin suna alfahari dashi matuka.

JARUMTA

Tana daya daga cikin Abinda mace ke so ga namiji, Sam basa son namiji lusari, Mara karfi, Don haka da yawan Mata su Kansu zaka ga sun fi son auren namiji Mai kirar karfi Wanda suke sanya ran jarumi ne domin shi zai iya dauke musu bukatarsu.

KYAU

idan akace kyau ga namiji ba Ana nufin kyawun fuska ba, Sau da dama Mata basu fiye kula da kyawun fuskar namiji ba, sunfi kula da kyawun halittar kamar yanda yawan cin maza suka kebance wasu abubuwan da suka fi bukata ga Mata, to su ma sunfi so suga namiji kamar haka.

MAI FADIN KIRJI

suna son namiji Mai Fadin kirji Wanda zai iya musu rumfa sosai, Kuma yana nuna cewa duk namiji Mai Fadin kirji ba za a samu rago ba, yana da kokarin dauke bukata.

MAI FADIN KUGU

shima yana da kokarin saukewa iyalinshi bukata gurin kwanciya ba tare da gaji yawa ba.

KARIN NI"IMA GA MATA

Ki samu kwakwa da kankana sai ki markadesu, ki samu Zuma Kadan kisa a ciki, sannan kisa a firj ya yi sanyi, shima sirrin ne.

Ki samu lemun tsami, ki rika wanke hammatarki tas, yana wanke hammata da kauda warinsa.


Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C