Abubuwan Da Masoya Ba Su So A Lokacin Zance (Hira)

Da yawan masoya na ƙorafi kan masoyansu duk da cewa matsalolin na da yawa amma zan ɗan yi duba akan wasu daga ciki.

Matsalar farko ita ce, wani namijin ya tsani jira yayin da ya je zance wajen budurwarsa, wannan daɗewar tana saka masa ƙuna cikin zuciya koda kuwa ya tawo tare da farin ciki; wasu mazan suna kasa jurewa sai su kiran hakan da wulaƙanci.

Yana da kyau ‘yan uwana mata da su yi haƙuri, su rage yawan jinkiri a lokacin da masoyansu suka zo domin faranta musu, don wata ta san zai zo, maimakon ta shirya tun kafin ya zo a a! Sai bayan ya zo zata fara shiryawa. Wata ma a lokacin za ta shiga wanka, sai ya gama ɓata lokacinsa idan yana da wani uzirin nasa ma sai ya haƙura ala dole tunda kin ɓata masa lokacin da ya gama lissafa abubuwan da zai yi a wannan ranar. Sai dai kawai ya danne zuciyarsa ya nuna miki hakan babu damuwa saboda yana son ki.

Ita kuwa ta yi ta washe baki babu wadda yake so sama da ke kuma ba za ki canja ba. Ki sani a duk lokacin da ya samu wadda ta fi ki iya soyayya da nuna kulawa barinki zai ya koma wurinta. Ko kuma ku yi ta samun matsala da shi saboda kina ƙona masa zuciya, koda a ce ba kya son sa akwai hanyoyin da za ki bi domin ku rabu lafiya.

A wani ɓangaren kuma wata macen takan fito zance tana taunar cingam (chewing gum), wanda maza da yawa sun tsani hakan, idan wani na son hakan, wani ba ya so, a nawa tunanin ma babu wanda zai so hakan, akan kanki ma idan kika yi tunani sosai za ki iya gane cewa matsayinki na ‘ya mace me tarbiyya wadda ta taso cikin al’adar malam Bahaushe yin hakan ba daidai ba ne.

Wani namijin daga wannan halin da ta nuna masa zai ji soyayyarta ta fita a ransa koda kuwa akwai sauran son da yake mata, yakan kasa sanin yadda zai fito ya faɗa mata matsalarta wanda ita a nata tunanin daidai ne.

Bari na daɗa hangawa a wani ɓangaren da yawan maza ba sa son suje zanje kuna hira kita ce masa (uhmm…), ko kuma (ina ji), shi ma hakan maza da yawa basa buƙatarsa shi namiji yana so ki buɗe baki kiyi masa magana kar ki ce ‘wannan ai wannan zubar da aji ne’ ko kaɗan da yawan matsaloli na soyayya akwai abunda in har kin yi su ba zubda aji ba ne.

Har ila yau su ma mazan, ya kama su fahimta cewar a cikin mata akwai waɗanda ba su da yawa daga halayenku. Wata macen bat a son maimaita zance kullum, ka zo zance hirar da za ka yi mata ta wancen zuwan da ka yi ne, yana da kyau kafin ka je zance ka tsara abinda za ka faɗa mata wanda za su sanyaya mata zuciya ya sa ta farin ciki ta tuna da kai yayin da ka koma gida.

Kar ka zo kai mata hiran Messi da Ronaldo ko Manchester da duk ma abinda ya shafi ƙwallo to mace ta tsane shi a wajen zance, duk da dai wasu matan su ma ‘yan ƙwallon ne amma dai da yawan mata basa buƙatar irin wa ‘yan nan hirar yayin da suke tare da masoyan su, ko hirar biki ko ta fim da dai sauran su, sai a tsaya ayi tunanin hirar da ta shafi masoyiyar ko masoyin wajen yaba halaye da kyawu da kuma yadda za a tsara rayuwa da sauransu, hakan shi yake ƙara ƙaunar juna tare da tuna juna a koda yaushe.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C