A Ina Matsalar Take Tsakanin Miji Da Mata?

Kun san duk lokacin da za a yi magana ko tattaunawa kan matsalolin aure a wannan zamani an fi ba wa mata laifufuka da dama na rashin kirki ana kallon su a matsayin mayaudara, marasa alkawari rashin tattalin miji, rashin tarbiya da ire-iren su dai.
Amma idan aka yi dogon nazari za a iske kaurin suna ne kawai, don za ka tarar wani namiji abin da yake yi ma iyalansa kare ba zai ci ba. Abin da ya kamata a zauna a bincika ana ba mai laifi laifinsa, wannan shi ne adalci.
Kaman yanda kowa ya sani mata da yawa suka jawo hakan, amma laifin wani bai dace a dora ma wani ba.
Wasu matan da zaran an ki ba su hakkinsu ba bincike wata fa za ka ga ta ce, to me ye amfanin an maka ka kai kara an ki bincike a gano mai laifi.
Wata fa ta balle daga nan ba ta ga auren ba ta ga zama gidansu, gidan miji ba dadi kuma gidansu ma haka, sai ta yi gaba an yi rashin uwa ta gari, sai wani gyaran Allah, wata kuma shi kenan ta zama daga wannan gidan sai waccan. Allah ya kyauta.
A dalilin haka yadda lamarin aure ya koma kaman yan zaman haya, muka dan yi wani bincike muka gano wasu boyayyun al’amura, kaman rashin kulawa kan lamarin abinci, daukar dawainiyar gida, makaranta, asibiti. Maganar sabulun wanki wanka omo man shafawa kawai ka da a je su hoda ko turare, wani namijin bai iya sayar wa matarsa komi, haba jamaa in ba tana kwakkwarar sanaa ba ya za ta yi da kanta.
In muka juya ta wajen mata kuma za mu ga ta su matsalar akwai mugayen kawaye, inda za ki ji kawa na shirya wa kawa mai aure yanda za ta yi da miji da iyayyensa, alhali ita ko aure ba ta yi ba, yadda za ta ce kar ki yarda kina musu girki kullum ba bauta ki ka zo yi ba.
In ya matsa ya dauko yar aiki ko kuma ya siwo a ci, haba yaruwa irin tarbiya kenan da ki ka samo daga gida, haka ki ka ga mama na yi har za ki bari wai kawa ta zo ta shirya miki yanda za ki tafiyar da gidanki. Wasu matan ga rashin godiya, kina zaune kina shan iska ba ki san ya ya samo kudin da ya sawo miki ba, amma ya kawo ki watsar ki gwasaleshi kaman kin aike shi ne.
Matsalolinmu a yau sun yi yawa maza da mata wannan zamani sai fa mun dage mu ji tsoron Allah musan aure nan dole ne, iyayyenmu ko ‘yan’uwa makusanta ba za su auremu ba, to sai mun je aure fa don shi ya haifemu domin muma mu haifi wasu, musan ibada ce ba neman kudi muka je ba.
Kuma yana da kyau mata ku ko yi sanaa wanda za ki yi ki taimaka wa kanki da ‘yan’uwa har mai gida. Ina ga zan dakata a nan mu tattauna a ba mai laifi laifinsa. 

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C