'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sha Uku Da Jikkata Mutum 7 a Katsina

A daren jiya Alhamis ne, yan bindiga bisa babura dauke da manyan makamai suka kai hari a garin Unguwar Gizo da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina, inda suka kashe mutum goma sha ukku har lahira, sun jikkata mutum bakwai yanzu haka suna kwance a asibiti. Kuma sun kwashe kayan abinci da dabbobin garin gaba daya.
Wani Mazaunin garin ya shaidawa RARIYA ta waya cewa "Yan bindigar sun zo garin da misalin karfe goma na daren jiya, sun kai su dari biyu kuma bisa babura, kowanne su dauke da bindigogi, suka fara harbe-harben kan mai uwa-da-wabi, inda suka harbe mutum ashirin, nan take sha ukku suka rigamu gidan gaskiya, bakwai kuma yanzu haka suna asibitin, domin cire masu harsashi. Sun balle shaguna da runbuna, kuma sun sace duk wata dabba a garin Unguwar Gizo.
Haka Kuma sun kai wadannan hare-haren a garuruwan Sabon Layin Mai Gora da Mai Gora inda suka balle shagunan masu saida kayan abinci suka kwashe na duka garuruwan. Har Ila yau sun je garin Mairuwa suka sace mutum ukku a daren jiya. Wadanan kauyukan duk suna karkashin karamar Faskari kuma sun kai farmakin ne tun karfe goma na har zuwa biyar asubahin yau Juma'a kuma babu jami'an tsaro da suka kawo masu dauki tsawon wadannan awowi da suka kwashe suna aikata ta'addanci wannan ta'addanci.
Kakakin rundunar 'yan Sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar wa manema labarai da wadannan hare-haren na daren jiya a kauyukan karamar hukumar Faskari.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C