Sirrin Mallakan Mijin Ki Cikin Sauki

'Yar Uwa Ga Naki Tsimin Rake Don Samun Dauwamamiyar Ni'ima
Yar uwa ya kamata ace kina da ni'ima a koda yaushe don zamantakewar aure tai kyau.
Yar uwa rashin ni'ima wadatacce babban matsalane ga mace ko kuma ma ga zamantakewar aure, domin wannan abun yana haifar da kiyayya, ita matan zataji mijin kamar yana takura mata ne, shima zai dunga jin zafi a gabansa wannan zai sa ko yana da bukatar kusantanta sai ya fasa.
Domin samun ni'ima yar uwa gwada wannan hadin.
Ruwan RakeKi: bare rake ki yanka gutsu-gutsu ki daka a turmi ko ki markada a ‘blander’ ki na yi ki na kara ruwa a dusar raken ki na matsewa. Idan kin sami ruwan rake kamar cikin jog daya. Sai ki sami ruwan tafasashshen baure jog daya. Sai ruwan jangari da jangagai da alewar mata da a ka tafasa su guri guda a ka tace su ma jog daya. Sai ki zuba wannan ruwayen naki a wuta ki zuba zuma kofi daya, ki yi ta dafawa har sai ruwan ya kone ya zama kamar cikin jug daya, sai ki sauke. Amma za ki sa kaninfari da kayan kamshi a dahuwar. Idan ya huce sai ki juye a abu mai kyau. Ba zai lalalce ba. Kullum ki sha ludayi daya. Zai ratsa jikinki ki sami dauwamammiyar ni’ima. Mai gida zai dinga jin dadinki ya na gamsuwa da ke sosai. Tsimin rake kenan.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C