Sace Mutane Da Rashin Tsaro, Ina Dan Nijeriya Zai Sa Kan Sa?

Kafin zuwan Coronavirus, alkaluman mu a jaridu sun koma ne kan sace mutane da karban dukiyoyin su wanda ya addabi Arewacin Nijeriya. Idan baku manta ba mun yi hasashen cewa matukar hukumomin tsaro basu dau mataki ba, ta'addancin zai iya wanzuwa a kowani sashi na kasar nan.
Da farko jihohin Zamfara, Katsina da kuma yankin Birnin Gwari na Kaduna suka yi ta fama da 'yan kidnafin, mahara da kuma masu sace dukiyoyin jama'a. Zuwa yanzu da muke magana, ta'addancin ya shiga kusa kowani jiha a Arewacin Nijeriya.
A jihata ta Adamawa, kananan hukumomi irin su Girei abun ya kai ga har ba a yin sati baka ji an sace mutum ba. Akwai wani farfesa a jami'ar Moddibbo Adama da aka dauke shi sau biyu ana karban kudi a wurin Iyalan sa.
A jihar Katsina, akwai basarake da bidiyon sa ya yadu a soshial midiya yana cewa bala'in da suke ciki a kauyuka irin su Batsari yafi musu annobar Korona. 'Yan ta' adda a Katsina sun kai ga har suna fitar da al'umma daga garuruwan su zuwa gudun hijira tamkar Boko Haram.
Yanzu abun bai tsaya a Zamfara da Katsina kawai ba, ya kai jihohin tsakiya irin su Nasarawa da Niger. A cikin watan Azumin nan gwamnan Nasarawa yayi ganawa na musamman da shugaban kasa akan 'yan ta'addan nan. Duk kokari na jami'an tsaron mu da yunkuri na gwamnati don kawo karshen 'yan ta'addan nan ya gaza matuka. Saboda ta'addancin a madadin ya ragu sai karuwa yake yi. Kusan ko ta wani bangare a Nijeriya abunda ake fama da shi kenan.
Masu ilimin tunanin dan Adam suka ce abubuwa uku ne suke sanya mutum aiwatar da ta'addanci: na farko rashin sanin illan abun da yake aikatawa, na biyu rashin damuwa da illan abunda yake aikatawa saboda wani dalili da ya tilasta shi zama dan ta'adda, na uku kuma samun biyan bukata wanda ya makantar da dan ta'addan barnar da yake yi.
A nan, gwamnati ya kamata ta yi nazarin karuwar ta'addanci a Nijeriya da idon basira. Dole sai an fahimci menene ke kawo karuwar ta'addancin saboda alkaluman bayanai sun nuna cewa sama da mutane miliyan tamanin a Nijeriya suna rayuwa ne cikin matsanancin talauci.
Kamar wannan bai ishe mu ba, sai ga cutar Korona a Nijeriya. Cutar da ta gagari kasashe masu karfin kiwon lafiya a duniya. Nan take gwamnati ta umurci a zauna a gida zuwa wani lokaci. Zama a gida zai iya kiyaye yaduwar cutar a tsakanin mutane, amman idan muka koma daya bangaren zamu ga yunwa da yake cikin gidan shima fitina ne mai zaman kansa.
Babu shakka wannan shine mafi munin lokaci ga dan Nijeriya. Dole gwamnati ta kara zuba hannu wajen taimakawa talaka a ko ina yake.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C