Rashin Yin Kyakkyawan Tsari Ne Ya Haifar Da Halin Da Makarantun Allo Ke Ciki_ Sanata Shekarau

A zantawarsa da manemna labarai tsohon gwamnan Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau sardaunan kano ya bayyana cewa rashin yin kyakkyawan tsari ne ya haifar da halin da makarantun allo suke ciki.
Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ya ji wani Gwamna daga Arewacin Nijeriya na cewa wai makarantun allon nan ba su tsinana wa kowa komai ba.
Shekarau, ya ci gaba da bayar da amsa cewa :- Ba dan wadannan makarantun allon da aka yi tsawon shekaru daruruwa ba, da shi wannan Gwamnan na Arewa dake kumfar baki akan makarantun allo bai iya karanta fatiha ba.
Tsari ne na shekaru da yawa daruruwa da aka yi saboda haka ba zai yiwu ba wani ko wasu su zo lokaci daya su ce za su rusa wannan tsarin ba, sai dai a hankali kuma sai an yi wa tsarin wani ingantaccen tsari na musamman tukuna.
Ya ce ” a lokacin da nake Gwamnan Kano hakika na fahimci abubuwa da yawa game da tsarin makarantun allo kuma na yi tsare-tsare da dama domin inganta tsarin na kuma samu nasara kwarai da gaske.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C