Makircin Jami'an Tsaro a Edo State

Bayan saka Dokan Hana fita daga karfe 8 zuwa 7 na safe sabida cutar covid-19 a Jihar Edo state mutane sunbi dokar kamar yadda gwamnati ta saka dokar
Amman wasu jami'an tsaro (police) abin baiyi musu dadi ba yadda suke bukatar mutane su karya dokan zama a gida su fito waje suyi awon gaba dasu Domin neman kudin beli
Sabida makirci irinna jami'an tsaron Najeriya suka nemi Mota kirar BUS wanda take dauke da fenti alamar motan haya ce
Su biyo ta babban titin Benin city wanda mutane suke yawan jirga jirga akansa, dai_dai lokacin da akan hana fita sai su fito suna nuna kamar motar haya ce, "Suna fadin ina mai zuwa Anguwa kaza ya shigo, sai bayan mutum ya shiga shikenan sun kama ka da sunan kai mai laifine
Daga karshe idan yan uwanka sunje Neman belinka, suce kai mai laifine ka taka doka ance a zauna a gida kaki kabi doka.
Ni kuma Isma'il Assalafiy Nace wannan rashin adalci ne, Zalinci ne wannan karara' Dole ne abar jama'a su fita su nemi Abinda Za suci, Yaushe za kace a zauna a gida kuma baka bayar da Abinda za'a ciba, Wannan zalinci ne, kuma sai Allah ya saka mus.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C