Kwanannan Gwamnati Zata Sallami Ma’aikatan N-Power

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin tarayya na shirin sallamar ma’aikatan N-Power 500,000 dake amfana da tsarin a yanzu.
A shekarar 2016 ne gwamnatin tarayya ta fito da tsarin dan rage radadin talauci da kuma tallafawa mutane fita daga kangin talauci, a shekarar 2018 an kara daukar wasu sabbin ma’aikatan N-Power wanda a yanzu sun cika shekaru 2 kenan.
Dama dai aikin na tsawon shekari 2 ne amma dibar farko a yanzu zun kai wajan watanni 40 suna aiki.
Salisu Na’inna Dabatta me baiwa Ministar Jinkai da kula da Ibtila’i shawara kan harkar watsa labarai ya labartawa Guardian cewa kwanannan za’a sallami duka ma’aikatan na N-Power.
Saidai be bayyana ranar da hakan zata faru ba.
Idan dai hakan ta tabbata to yawan marasa aikin yi a Najeriya zai karu duk da dai cewa ana tunanin wata kila gwamnatin ta sake daukar wasu sabbin ma’aikatan.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C