Gyaran Kasa Akwai Wahala Inji Ministan Yada Labarai Lai Mubammad

Ministan yada labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa shugaban kasa,Mubammadu Buhari ya Dora Najeriya a turbar ci gaba me dorewa.
Lai Mubammad ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja kan cikar shugaba Buhari shekaru 5 akan karagar Mulki da kuma shekara 1 kan zangonshi na biyu.
Yace matakan da shugaban kasar ya dauka ne yasa Najeriya ta kama hanyar kaiwa ga tudun mun tsira.
Yace saboda yanda ‘yan Najeriya suka gamsu da aikin shugaban wajan samar da tsaro, habaka tattalin arziki da yaki da rashawane yasa suka sake zabarsa a shekarar 2019.
Yace shekara 1 bayan zaben gashi shugaba Buhari na ya dora Najeriya kan hanyar zuwa mataki na gaba.
Yace akwai tsari me kyau na magance matsalar wutar lantarki da ta ki ci taki cinyewa a Najeriya,
Sannan kuma ya godewa ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatin shugaban kasar, yace akwai kuma tsarin habbaka noma na musamman wanda nan gaba zasu yi magana akanshi shi da ministan harkar Noma.
Yace Najeriya ta kama hanyar zama kasa me ciyar da kanta.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C