Da Dumi-Dumin Sa_Jami'an farin kaya na DSS sun cafke wanda yayi garkuwa da jikan Sheikh Dahiru Bauchi

Hukumar jami'an tsaro ta farin kaya na jihar Bauchi, ta bayyana sun cafke wani matashi mai suna Umar Ahmad wanda ake zargin yin garkuwa da jikan fitaccen malami Sheikh Dahiru Bauchi.
Hukumar tace tayi nasarar kwato yaron dan shekaru uku da haihuwa daga matashin dan shekaru 27 da haihuwa wanda aka biya diyyar Miliyan 2.5.
Yaron dai an yi garkuwa da shi ne tun ranar 22 ga watan Mayun da muke ciki.
Shugaban hukumar ta DSS Muhammad Alhassan, yace sun samu nasarar kama wanda ake zargin ne tare da hadin guiwar 'yan sandar Jihar Kano.
Alhassan ya kara da cewa wanda ake zargin da farko ya bukaci sai an bashi Miliyan 10 daga baya kuma ya rage zuwa Miliyan 6.
"Kai tsaye muka shiga bincike bayan da muka samun rahoton cewa wanda ake zargin yana zaune a Otal din Liberty daki na 37 dake rukunin gidaje na Sabon Gari.
"Da muka kai sumame cikin Otal din mun samu nasarar kwato yaron tare da kama wanda yayi garkuwa da shi, kuma an ciro kudin daga asusun bankin mai laifin".
Yace mai lafi za a mika shi ga jami'an'yan sanda domin ya ke masa hukunci.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C