Bana Cikin Tafiyar Gwamna El-Rufai_Inji Hadiza El-Rufai

Hadiza El-Rufai, matar gwamnan jihar Kaduna, ta ce bata cikin tafiyar gwamnatin mijinta.
A yayin magana a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, Hadiza ta ce sau da yawa tana nesanta kanta daga yin tsokaci a kan zantukan shugabanci da siyasa.
Kamar yadda ta sanar, ba kamar gwamnoni ba da sauran masu mulki da aka zaba, bata karkashin wani ofishi da tayi rantsuwa, don haka kai tsaye take bayyana matsayarta a kan al'amura da dama.
Kamar yadda ta kara da cewa, shafin ta na kafar sada zumuntar zamani tana koyar da yare ne da sauransu.
"Kun taba ganin na saka 'matar gwamna' a bayanai na? Shafina na koyon yare ne da sauran al'amura marasa nauyi. Bana wallafa a kan shugabanci da siyasa. Duk da ina auren gwamna, bana cikin gwamnatinsa. Ban yi rantsuwa ba," tace.
Wannan tsokacin nata ya zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a kan kisan da 'yan bindiga suka yi wa jama'a a yankin kudancin jihar Kaduna.
Matar gwamnan ta shiga kanun labarai a watan Afirilun da ya gabata, bayan zarginta da aka yi da goyon bayan dan ta Bello Rufai bayan tsokacin da yayi na nuna cin zarafi ga mahaifiyar wani a Twitter.
Daga baya Hadiza ta bada hakuri a kan wallafarta tare da jaddada cewa bata goyon bayan cin zarafi kowanne iri ne.
"Na ga yadda wallafa ta fito. Ina bada hakuri ga wadanda na saba wa. Ina sake jaddada cewa bana goyon bayan cin zarafi kowanne iri," kamar yadda ta wallafa.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C