Bakin Tarihi a Gwamnatin Shugaba Buhari Mai Gaskiya

Rashin Tsaron Da Ya Faru A Gwamnatin Jonathan Shi Yake Faruwa A Gwamnatin Buhari A Yanzu.
Kamar yadda jaridar RARIYA ta ruwaito wannan labarin cewa 'Yan ta'adda sun sa mazauna yankin Sabon-Birni dake jihar Sokoto yin gudun hijira.
Wannan bakin tarihi ne da ya kamata ya tashi hankalin duk wani mai son shugaba Muhammadu Buhari Maigaskiya tsakaninsa da Allah, abinda muka gani ya faru a gwamnatin Jonathan shine yake faruwa yanzu a gwamnatin Baba Buhari.
Na ga wani Labari wai yanzu haka Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da tawagarsa yana kan hanyar zuwa garin Sabon Birni inda aka yiwa mutane kisan kare dangi yammacin jiya.
Ziyarar gani da ido duk shirmene a tawa fahimtar, daukar matakin ramuwar gayya mai tsauri tare da isar da yaki ga 'yan ta'adda a duk inda suka buya shine abin bukata, kuma ance yau ma sai da 'yan ta'addan suka sake dawowa garin suka hana zaman makoki bayan sunyi ta'addancinsu jiya, gaskiya wannan abin kunya ne garemu da muka kafa wannan gwamnatin.

Comments

Popular posts from this blog

ABUBUWAN DA MACE TAFI SO A TABA MATA

Burin Kowani Da Namiji Ya Auri Budurwa

ABUBUWAN DA AKE BUKATA GA WANDA ZAI NEMI AIKIN N-Power RUKUNIN C